Sport
Dollar
39,0355
0.29 %Euro
44,1457
0.22 %Gram Gold
4.144,3200
0.51 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Guardiola ya kasance mai son aiki da ƙaramar tawaga, amma yawan 'yan wasansa da suka je jinya ya kassara tagomashin Manchester City a kakar bana.
Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa zai zaɓi barin aiki a ƙungiyar da a ce ya yi aiki da tawaga mai tarin ‘yan-wasa a kaka mai zuwa.
Kocin na City ya fara ƙoƙarin sake gina tawagarsa, bayan da kakar bana ta zo ƙarshe ba tare da sun lashe wani kofi ba. hakan ya faru ne a karon farko tun shekarar 2017.
Guardiola ya fada ranar Talata cewa zai ƙauracewa ƙungiyar maimakon atilasta masa jagorantar tawagar da tara ‘yan-wasa da yawa.
“Na faɗa wa kulob ɗin cewa ba na son haka. Ba na son a ce na bar 'yan wasa biyar ko shida a gida,” in ji Guardiola bayan wasan da tawagarsa ta yi nasara da 3-1 kan Bournemouth.
Ya ƙara da cewa, “Ba na son hakan. Sai in yi murabus. Ku rage yawan 'yan wasa; zan zauna. Ba zai yiwu ba a ce na tafi wasa na bar 'yan wasa a wajen filin wasa saboda ba su samu damar buga wasa ba.”
Ƙaramar tawaga
Pep Guardiola ya bar James McAtee, Savinho da Rico Lewis daga tawagarsa a wasan gasar Firimiya na ranar Talata.
Haka kuma ya yanke irin wannan shawarar mai wahala a wasan ƙarshe na gasar FA Cup da suka yi rashin nasara a hannun Crystal Palace ranar Asabar.
A al'adarsa, Guardiola yana son aiki da ƙaramar tawaga, amma raunin da 'yan wasansa suka samu a wannan kakar — ciki har da tiyatar gwiwa da aka yi wa Rodri, ya shafi ƙarfin City na riƙe kambunta na bara.
Manchester City ta kashe fiye da dala miliyan 200 a watan Janairu don ƙoƙarin ceto kakar bana, inda suka sayo Omar Marmoush, Nico Gonzalez, Abdukodir Khusanov da Vitor Reis.
Bayan kammala kakar bana, ana sa ran Guardiola zai yi babbar sayayya, yayin da Kevin De Bruyne zai bar kulob ɗin, kuma Kyle Walker ma na iya tafiya.
Comments
No comments Yet
Comment