Sport
Dollar
38,8410
-0.04 %Euro
43,9735
0.11 %Gram Gold
4.109,9100
0.02 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Masu bibiyar ƙwallon ƙafa a Amurka sun tofa albarkacin bakinsu kan kalaman ɗan ƙwallon Inter Miami ta Amurka, Lionel Messi da ke zargin alƙalan wasa a gasar MLS ba su iya alƙalanci ba.
Gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, Lionel Messi ya zargi alƙalan wasa a babbar gasar ƙwallo ta Amurka, MLS da nuna rashin sanin dokokin ƙwallo yayin aikinsu.
Messi ya yi wannan zargi ne bayan wani wasa da ƙungiyarsa ta Inter Miami ta kara da Orlando City, inda suka sha kaye da ci 3-0.
Da yake magana kan abubuwan da suka faru a wasan, Messi ya ce alƙalin da ya yi hukunci a wasan 'bai san doka ba!', inda ya yi kira da hukumar gasar da ta “duba ƙa’idojin alƙalancin ƙwallo'.
Ɗan wasan ɗan asalin Argentina ya bayyana ɓacin-ransa kan abubuwan da ke faruwa a makonnin baya-bayan nan a gasar, sakamakon yadda ƙungiyarsa ta sha kaye sau 5 cikin wasanni 7 a duka gasanni.
Martanin masana ƙwallo
A Fabrairu, cikin wani wasan Inter Miami da New York City da aka tashi canjaras, an ga Messi yana jan wuyar kocin ƙungiyar da suka fafata da su.
Sannan a ƙarshen wasan Messi ya ƙalubalanci alƙalan wasan cikin fushi, idan da ƙyar aka ceto shi daga samun jan kati.
Taylor Twellman, wani tsohon ɗan ƙwallon tawagar Amurka ya soki kalaman na Lionel Messi, inda ya ce sam ‘ba za a karɓi wannan suka’ ba.
Twellman ya ce an ci su ‘ƙwallo 20 a wasanni shida!’, wannan ba uzuri ne ba’, inda yake yin tambaya kan madogarar sukar da Lionel Messi ya yi wa alƙalai, duba da yadda ƙungiyarsa ta rasa tagomashi.
Inter Miami dai ta fara shekarar nan da sabon koci, Javier Mascherano, inda suka fara samun nasara.
Amma sai ga shi sun sha kaye sau 5 a wasanni 6, inda aka ci su zunzurutun ƙwallaye 20 a wasa 5 kacal, kuma aka fitar da su daga gasar CONCACAF Champions Cup.
Comments
No comments Yet
Comment