Dollar

38,8597

0.07 %

Euro

43,9172

0.35 %

Gram Gold

4.109,1300

1.97 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya bayyana cewa har yanzu ƙofarsa a buɗe take kan farauto tauraron ɗan-wasa Erling Haaland daga Manchester City.

Shugaban Barcelona ya ce bai hakura da neman ɗauko Haaland ba

Shugaban ƙungiyar Barcelona ta Sifaniya, Joan Laporta ya bayyana cewa ‘ba abin da ba zai iya faruwa ba’, game da batun ɗauko tauraron ɗan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaland.

Laporta ya ce har yanzu ƙofar Barca a buɗe take ga ɗan wasan, inda yake nuna batun sayo Haaland daga City abu ne mai yiwuwa.

Tun a 2024 ne rahotanni suka bayyana cewa Laporta ya ƙuduri aniyar ɗan ɗan wasan wanda ɗan asalin Norway ne da ya yi suna wajen cin ƙwallaye.

Amma ko a lokacin Barcelona tana cikin matsin kuɗi, batun da han yanzu bata fita daga ciki ba. Ga shi kuma ɗan wasan mai shekaru 24 zai yi tsada a kasuwa.

Me Laporte ya faɗa?

Sai dai watanni kaɗan bayan Barca ta nuna kwaɗayinta kan Haaland, ɗan-wasan ya rattaba hannu kan sabuwar kwantiragi da Man City, wadda ta kai tsawon shekaru 10 rigis.

Kwantiragin na nufin Haaland zai zauna a Man City har zuwa bazarar 2034. Amma duk da haka shugaban na Barca bai cire rai kan yiwuwar farauto Haaland ba.

Rahotanni sun ambato Joan Laporta yana magana da gidan talabijin na TV3, ya ce, “Shin Barcelona za ta iya sayo Erling Haaland? Babu abin da ba zai iya faruwa ba. Amma ba hakan ne a gabanmu ba a yanzu. Kuma dai bai daɗe da samun sabuwar kwantiragi ba.”

Kalaman Laporta hujja ce da ke nuna cewa Barca ba ta fitar da tsammani ba, kuma ba ta fasa mafarkin ganin Erling Haaland ya taka mata leda ba.

A yanzu dai Barcelona ta yi nasarar ɗaga kofunan La Liga da na Copa del Rey, duk da akwai wasa ɗaya da ya rage musu a kakar 2024-25, wanda za su buga ranar 25 ga Mayu tare da Athletic Club.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#