Sport
Dollar
38,8701
-0.02 %Euro
43,9806
0.09 %Gram Gold
4.125,7300
0.41 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kyautar ta shekarar 2025 za a gabatar da ita ne ranar 22 ga watan Satunba a birnin Paris, in ji sanarwar da hukumar UEFA ta fitar ranar Litinin.
Bana bikin ba da kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa ta Ballon d’Or za ta ba da damar samun ƙarin mata da za a gabatar domin samun damar cin gasar.
Bikin ba da kyautar na shekarar 2025 za a yi shi ranar 22 ga watan Satumba a Paris, in ji hukumar ƙwallon ƙafar Turai UEFA a sanarwar da ta fitar ranar Litinin.
A wannan karon bikin ba zai ci karo da lokacin wasannin ƙasashe na ƙwallon ƙafar mata a lokacin da mata suke wakiltar ƙasashensu ba.
“Muna alfaharin faɗaɗa matakan kyaututtuka uku cikin kyauttukan da muke bai wa mata ‘yan ƙwallo,” in ji UEFA, wadda tun shekarar da ta gabata ne ta fara bai shirya bikin ba da kyaututtukan tare da kamfanin da ke buga mujallar “France Football”.
Sabbin kyauttuka
Mata ‘yan wasa da koca-kocai sun soki masu shirya bikin a cikin shekaru biyun da suka wuce yayin da yawancin su ba su iya kasancewa a Paris domin halartar bikin.
Waɗannan bukukuwan an yi su ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2023 da kuma ranar 28 ga watan Oktoban shekarar 2024— da yammacin ranakun Litinin a makonnin da babu wasannin maza na Gasar Zakarun Turai ko na ƙasashe.
Ranar 22 ga watan Satumba za ta sake kasancewa ranar Litinin a wani makon da ba shi da wasannin Champions League ko na ƙasashe. Kazalika makon ba shi da wasannin mata.
Waɗanda suka ci kyautar Ballon d’Or a bara daga ƙasar Sifaniya suke: ɗan wasan tsakiyar Manchester City midfielder Rodri da kuma ‘yar wasan tsakiyar Barcelona Aitana Bonmatí. Ita ce ta na shekarar da ta gabaci bara.
Sabbin matakan kyautar mata za su karrama ‘yar wasa mai ƙananan shekaru da ta fi ƙwarewa da golar da ta fi ƙwarewa da kuma wadda ta fi zura ƙwallo a raga a kulob ko ƙasarta.
A cikin watan Agusta ne dai za a bayyana sunayen waɗanda ake sa ran za su ci kyaututtukar, in ji, UEFA.
Comments
No comments Yet
Comment