Sport
Dollar
39,0330
0.28 %Euro
44,0488
-0.01 %Gram Gold
4.140,4200
0.42 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce ya ji daɗin taron bayan da kwanton ɓaunar Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, wanda ya yi kamar yadda Shugaban Amurka ya yi wa Shugaban Yasar Ukrain Volodymyr Zelenskyy da suka gabata
Kafin taron ranar Laraba a Fadar White House, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi fatan amfani da ƙwarewarsa ta iya sasanci don gyara abin da ya kira kuskuren fahimtar Afirka ta Kudu da Amurka ta yi — tare da tattaunawa kan sabbin yarjejeniyoyin kasuwanci.
Amma maimakon haka, ya fuskanci wani yanayi mai sarƙaƙiya daga Shugaba Donald Trump, wanda ya yi kama da abin da ya faru da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy watanni uku da suka gabata.
Trump ya nuna masa wani bidiyo da ya ce hujja ce ta “kisan kiyashi na fararen fata” da ake yi wa fararen fata a Afirka ta Kudu.
Shugaban Amurka ya kuma nuna wasu labaran jaridu da ya ce suna goyon bayan ikirarin nasa – duk da cewa ɗaya daga cikinsu ya nuna hoton tashin hankali a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ba Afirka ta Kudu ba.
Irin wannan yanayi ne da mutanen Afirka ta Kudu suka yi fargabar cewa Shugaba Ramaphosa zai fuskanta daga “bakin Trump marar linzami,” kamar yadda wata jaridar Afirka ta Kudu ta bayyana.
Ga wasu muhimman abubuwan da suka fito daga taron ofishin Oval.
Nutsuwar Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu ya shahara wajen ƙwarewarsa ta sasanta rikice-rikice, inda ya yi suna a matsayin babban mai sasanci a tattaunawar shekarun 1990 da ta kawo karshen tsarin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.
Tashin hankali na diflomasiyya kafin taron ya sa Ramaphosa ya yi tsammanin wani yanayi mai sarƙaƙiya. A makon da ya gabata, Amurka ta karɓi wasu fararen fata kimanin 50 daga Afirka ta Kudu da aka ba su matsayin 'yan gudun hijira a matsayin wadanda aka yi wa “kisan kiyashi na fararen fata.” Wannan batu ya fuskanci suka sosai, har da gwamnatin Afirka ta Kudu.
A yayin da kyamarorin talabijin ke ɗaukar hotunan yadda zaman ke kayawa, Ramaphosa ya ci gaba da kasancewa cikin nutsuwarsa kuma ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen kauce wa rikici.
Bai fada tarkon kalaman mai masaukinsa ba, kuma ya tsaya kan dabararsa inda ya yaba, har ma ya yi barkwanci cewa ba shi da jirgin sama da zai ba Trump a matsayin kyauta.
Barkwancin Ramaphosa kan jirgin sama
A kan batun kyautar jirgin sama da Qatar ta ba Shugaban Amurka kwanan nan, Ramaphosa ya rage zafin yanayin taron da barkwanci, yana cewa, “Yi hakuri, ba ni da jirgi da zan ba ka.”
“Na so a ce kana da shi. Zan karɓa,” Trump ya mayar da martani, wanda ya sa aka fashe da dariya a ɗakin taron.
Kasar Gulf mai arziki ta ba da wannan jirgin sama mai darajar dala miliyan 400 don ya zama sabon jirgin saman Shugaban Ƙasa na Air Force One.
Firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani ya kare wannan kyauta a matsayin “musayar alaka tsakanin kasashe biyu.”
Babu wata yarjejeniya ta tattalin arziki da aka sanar
Ramaphosa ya tafi Amurka da fatan cim ma sabbin yarjejeniyoyin kasuwanci kuma ya bayyana cewa a shirye yake don wannan tattaunawa.
Trump ya dakatar da duk wani tallafin Amurka ga Afirka ta Kudu kuma a watan Maris ya kori jakadanta saboda ya kira manufofin Trump a matsayin “mayar da martani na wariyar launin fata ga ƙaruwar bambancin ƙabilanci a Amurka.”
Afirka ta Kudu ta kuma fusata Fadar White House kan yunƙurinta na kai ƙara a Kotun Duniya kan zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza.
Da yake magana da manema labarai bayan barin Fadar White House, Ramaphosa ya ce ya gamsu da taron. Ya ce kasashen biyu sun amince su tattauna kan albarkatun ma'adinai masu muhimmanci a Afirka ta Kudu, amma bai bayar da cikakken bayani ba.
Ramaphosa ya ce har yanzu yana sa ran Trump zai halarci taron G20 a Johannesburg a watan Nuwamba.
An kuma gabatar da wani shirin kasuwanci da zuba jari, wanda ya haɗa da sayen iskar gas mai ruwa daga Amurka, in ji ministan kasuwancinsa.
Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashen da ke fuskantar manyan harajin shigo da kaya da Amurka ta ƙaƙabawa a karkashin manufofin kasuwanci na Trump. Babu wata yarjejeniya da aka sanar kan harajin bayan taron shugabannin biyu.
Tambayar Elon Musk
Dan asalin Afirka ta Kudu Elon Musk, wanda ke cikin ofishin Oval, ya kasance babban mai goyon bayan ikirarin “kisan kiyashi na fararen fata,” wanda ya samu karbuwa sosai a duniya.
Ya taba ikirarin cewa Starlink, kamfanin sadarwar tauraron ɗan’adam nasa, an hana shi aiki a Afirka ta Kudu saboda shi ba baƙar fata ba ne, wani zargi da jami’an Afirka ta Kudu suka musanta.
Dokokin Bunkasa Tattalin Arzikin baƙar fata na gida suna bukatar lasisin sadarwa na kasashen waje su sayar da kashi 30% na hannun jarinsu ga kungiyoyin da aka danne a tarihi.
Wakilan Afirka ta Kudu da suka gana da Trump sun hada da Johann Rupert, wani ɗan Afirka ta Kudu mai arziki kuma attajirin kayan alatu mafi arziki a kasar.
“Muna bukatar Starlink a kowace tashar ‘yan sanda ta gida,” Rupert ya fada wa Trump a wani yunkuri na magance damuwar Musk.
Kafin tafiyar Ramaphosa, gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi nuni da cewa za ta yi sassauci ga kasuwancin Musk, ciki har da bayar da lasisin aiki ga kamfanin motarsa, Tesla.
Batun ƙarar Afirka ta Kudu a ICJ kan Isra'ila bai zo ba
“Ramaphosa ya kauce wa harsashi,” kamar yadda wata jaridar Afirka ta Kudu ta bayyana taron ofishin Oval. Kafofin watsa labarai na gida suna ganin ya fita ba tare da wata illa ba daga wannan rikici mai ban mamaki.
Shugaban Jam’iyyar Democratic Alliance, wata jam’iyya da fararen fata suka fi rinjaye a gwamnatin hadin gwiwar Ramaphosa, wanda kuma shi ne ministan noma, John Steenhuisen, ya kasance cikin tawagar. Ya bayar da muhimmin goyon baya ga gwamnatin Afirka ta Kudu.
Wani taro na sirri bayan rikicin ofishin Oval bai tabo batun ƙarar Afirka ta Kudu a Kotun Duniya ba, inda Pretoria ke zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza.
Duk da rikicin da ya faru yayin taron da Trump, Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya yi kokarin rage tasirin abin da ya faru.
“Kun yi tsammanin ganin rikici da wani abu mai girma ya faru,” Ramaphosa ya fada wa manema labarai daga baya. “Yi hakuri da muka ba ku kunya kadan.”
Comments
No comments Yet
Comment