Dollar

38,9252

0.13 %

Euro

44,0379

-0.13 %

Gram Gold

4.132,5200

-0.25 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kamen na zuwa ne bayan an samu tashin hankali mafi muni tsakanin maƙwabtan masu hamayya tun rikicin da suka yi kai-tsaye a shekarar 1999.

India ta kama ‘yan ƙasarta 11 bisa zargin yi wa Pakistan leken asiri

Hukumomin Indiya sun kama mutane 11 ‘yan ƙasar kan zargin yi wa Pakistan leƙen asiri bayan an samu tashin hankali mafi tsanani tsakanin ƙasashen biyu cikin gomman shekaru, kamar yadda rahotanni daga ƙasar masu ishara ga ‘yan sanda suka ruwaito.

Kafar NDTV ta ruwaito ranar Litinin cewa hukumomi sun kama waɗanda ake yi wa zargin kasancewa “‘yan leƙen asiri” a jihohin Haryana da Punjab da kuma Pradesh da ke arewacin ƙasar.

Babban daraktan ‘yan sandan Punjab, Gaurav Yadav, ya bayyana a ranar Litinin cewa, jami’ansa sun kama mutum biyu “ da ke da hannu wajen kwarmata bayanan soji".

‘Yan sanda sun samu "bayanai masu tushe " kan cewa mutanen biyu suna da hannu wajen kwarmata bayanan sirri da ke da alaƙa da hare-haren New Delhi can cikin ƙasar Pakistan a daren 6 zuwa 7 na watan Mayu.

Bincike farko-farko ya nuna cewa sun [yi] “magana kai-tsaye” da jami’an da suke magana da su a hukumar leƙen asirin Pakistan (ISI), kum [sun] "tura muhimman bayanai game da rundunar sojin Indiya," in ji Yadav.

Pakistan ba ta yi tsokaci game da zargin leƙen asirin ba.

Yayin da hukumomin Indiya ba su ba da cikakken bayani ba tukunna game da zargin leƙen asirin, wani jami’in ‘yan sanda a jihar Haryana ya bayyana wa Hindustan Times cewa an kama mutanen ne saboda amfani da kafafan sada zumunta.

“Wannan ma (wani nau’i ne) na yaƙi, inda suka (Pakistan) yi ƙoƙarin yaɗa manufarsu ta hanyar amfani da fitattu [a kafofin sada zumunta],” kamar yadda jami’in ‘yan sanda Kumar Sawan ya bayyana.

Aƙalla mutum 60 ne suka mutu a rikicin da aka yi da farkon wannan watan, wanda ya faru sakamakon wani harin da aka kai ranar 22 ga watan Afrilu a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya, wanda New Delhi ta zargi Islamabad da taimaka wa, wani zargin da Pakistan ta ƙaryata baki ɗaya.

An kama mai labaran tafiye-tafiye

A jihar Haryana, ‘yan sanda sun kama wata mai wallafa labarai a intanet kan tafiye-tafiye a makon da ya gabata kan zarge-zarge masu kama da wannan.

‘Yan sanda sun ce matar da ake zargin ta yi balaguro zuwa Pakistan aƙalla sau biyu kuma tana magana da wani jami’i daga ofishin jakadancin ƙasar, kamar yadda rahotanni daga ƙasar suka bayyana.

Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da wani ɗalibi da wani mai gadi da kuma wani ɗan  kasuwa.

Kafar India Today news ta ba da rahoton cewa an kama wasu mutane 11. Ta ce waɗanda ake zargin "an janyo hankalinsu cikin harkar leƙen asirin ne ta kafafen sada zumunta da kuɗi da alƙawurran ƙarya da kuma tafiye-tafiye zuwa Pakistan".

Kamen na zuwa ne bayan tashin hankali mafi tsanani tsakanin makwabtan masu hamayya tun yaƙin da suka yi kai-tsaye a shekarar 1999.

An cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kwanaki huɗu na hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi da manyan bindigogi waɗanda suka janyo fargabar ɓarkewa yaƙi.

Rikicin Kashmir

Indiya da Pakistan suna rikici kan Kashmir da ke cin gashin kanta a da tun lokacin da suka sami ‘yancin kai daga mulkin Birtaniya a shekarar 1947, inda iyaka ta raba iyalai  da juna.

‘Yan tawaye daga ɓangaren da ke ƙarƙshin ikon Indiya na yankin sun kasance suna tayar da ƙayar baya tun shekarar 1989, suna masu neman ‘yancin kai ko kuma a haɗa su da Pakistan.

New Delhi, wadda ta tura dakaru 500,000 a Kashmir ɗin da ke ƙarƙshin ikon Indiya inda mafi yawan mutanen wajen Musulmai ne, ta bayyana tawayen da ake yi a Kashmir a matsayin "ta’addancin da Pakistan ke mara wa baya ", zargin da Pakistan ta musanta.

A cikin ‘yan makonnin nan, gwamnatin Modi ta zafafa matsin lambarta kan ƙungiyoyin addinin Musulunci da adabi da makarantu, lamarin da ke janyo tashin hankali.

Kazalika, Indiya ta ba da takardar shaidar zama ga baƙi 82,000 a garin da ake rikici a kai, lamarin da ya janyo fargaba game da shirin sauya mutanen wajen da gangan.

Bayan harin Pahalgam, an kama sama da mutum 1,500 a ɓangaren Kashmir da ke ƙarƙshin ikon Indiya.

Kazalika rahotanni da ke nuna yadda gungun masu tsattsaurar ra’ayin addinin Hindu ke far ma Musulman Kashmir—yawancinsu ɗalibai— a biranen Indiya sun bayyana.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#