Sport
Dollar
38,8031
0.05 %Euro
43,1758
0.21 %Gram Gold
4.025,5600
-0.24 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Sakamakon yanayin inda kasar ta ke, ana yawan samun walkiya akai-akai inda a bara ta kashe kusan mutane 300.
Akalla mutane 13 ne suka mutu sakamakon ibtila’in walkiya da aka yi a wasu sassan ƙasar Bangaladesh a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar asarar rayuka sakamakon ibtila’in a ƙasar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu da gidan talabijin na Channel 24 suka bayyana.
Walƙiyar ta kashe mutane tara waɗanda suka haɗa da yaro ɗaya da wasu manoma a gabashin yankin Brahmanbaria da ke tsakiyar Kishoreganj a ranar Lahadi.
Kazalika, an rasa mutum ɗaya a kowacce daga gundumomin Chapaiwabganj, da Naogaon, da Sherpur da kuma Habiganj, in ji Channel 24.
Aƙalla mutane huɗu ne suka jikkata a ibtila’in tsawar
Tun da farko dai Hukumar Hasashen Yanayi ta Bangladesh (BMD) ta fitar da sanarwar hasashen za a samu tsawa a sassa da dama na ƙasar a yammacin Lahadi a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tsananin yanayin zafi a faɗin kasar, ciki har da babban birnin kasar, Dhaka.
Faɗakarwa don ceton rayuka
A ranar 28 ga Afrilu, aƙalla mutane 17 ne suka mutu a gundumomi 7 na ƙasar sakamakon walƙiya, lamarin da ya kai ga faɗakar da jama'a don ceton rayuka.
Wata ƙungiyar sa kai mai suna ‘'Save the Society and Thunderstorm Awareness Forum’’ da ke aikin wayar da kan jama’a game da walƙiya, ta bayyana damuwar a cikin wata sanarwa da ta fitar kan yadda mutane da dama ke mutuwa sakamakon walƙiya.
Kabirul Bashar, shugaban ƙungiyar kuma malami a jami’ar Jahangirnagar, ya ce sama da kashi 70 cikin 100 na mutanen da ke mutuwa sakamakon ibtila’in walƙiya, manoma ne da ke aiki a gonaki.
Ya kuma jaddada muhimmacin wayar da kan jama’a domin ceton rayuka, duba da cewa babu yadda za a yi a hana walƙiya afkuwa.
Bisa ga alƙaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, kimanin mutane 300 ne ke mutuwa a kowace shekara sakamakon tsawa a Bangladesh. A bana mutane 67 ne suka mutu sakamakon tsawa daga watan Janairu zuwa 30 ga Afrilu, yayin da mutane 297 suka mutu a bara.
Ana yawan samun mace-mace daga watan Afrilu zuwa Yuni da kuma ƙaruwar adadin waɗanda ke jikkata, tun dai a ranar 1 ga Afrilu, hukumar BMD ta fitar da sanarwar gargaɗi game da tsawa a Bangladesh.
Comments
No comments Yet
Comment