Dollar

38,7786

0.39 %

Euro

43,8944

0.27 %

Gram Gold

4.147,5900

1.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da maƙwabtan biyu waɗanda duka ke da makaman nukiliya ke ci gaba da kai wa juna hari.

Pakistan ta ce ta harbo jirage marasa matuƙa 77 na Indiya a cikin kwana biyu

Majiyoyin sojan Pakistan sun tabbatar da cewa an harbo jiragen Indiya 77 marasa matuƙa a cikin kwanaki biyu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da maƙwabtan biyu waɗanda duka ke da makaman nukiliya ke ci gaba da kai wa juna hari .

“A ranar 8 ga watan Mayu, Pakistan ta harbo jiragen Indiya 29 marasa matuka, yayin da aka lalata jirage marasa matuka 48 a cikin dare,” kamar yadda tashar talabijin ta PTV News ta Pakistan ta bayar da rahoto.

Adadin wadanda suka mutu a arangama mafi girma tsakanin Indiya da Pakistan a cikin shekaru da dama ya wuce 50, inda kowace kasa ke zargin maƙwabciyarta da amfani da jirage marasa matuƙa wurin kai hare-hare.

 Ta wani ɓangaren kuma ‘yan sanda a yankin Kashmir na Pakistan sun ce harin da Indiya ta kai a cikin dare ya kashe fararen hula biyar, a daidai lokacin da maƙwabtan biyu suka shafe kwanaki suna musayar wuta.

Jami'in 'yan sanda Adeel Khan da ke gundumar Kotli ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, "Sojojin Indiya sun yi luguden wuta kan wasu fararen hula, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyar, ciki har da wata yarinya 'yar shekara biyu, tare da raunata wasu goma sha biyu."

Wani babban jami'in gwamnati da ke Muzaffarabad ya tabbatar da mutuwar.

 “ A martanin da ta mayar, rundunar sojin ta Pakistan ta mayar da martani ta hanyar harin ramuwar gayya kan wasu wuraren da jami’an tsaron Indiya suke a kan iyakar da ta raba Kashmir da Indiya.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#