Dollar

40,3630

0.13 %

Euro

47,0061

0.32 %

Gram Gold

4.355,4200

0.67 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Fafaroma ya bayyana “kusancinsa, kulawa, addu’a, goyon baya, da kuma burinsa na yin duk mai yiwuwa don cim ma ba kawai tsagaita wuta ba, har ma da kawo karshen wannan masifa,” ya kara da cewa.

Fafaroma Leo: Lokaci ya yi na dakatar da kisan da ake yi a Gaza

Fafaroma Leo ya yi kira da a kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa a Gaza ba tare da ɓata lokaci ba, yana Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan Cocin Katolika na Holy Family a matsayin abin da ba za a iya yarda da shi ba, in ji Cocin Latin ta Birnin Ƙudus.

Bayan ya ziyarci Cocin Katolika na Holy Family, wanda shi ne kadai cocin Katolika a Gaza, tare da shugaban cocin Orthodox na Girka, Theophilos III, Cardinal Pierbattista Pizzaballa ya bayyana cewa, faforoma ya kira shi kai tsaye yayin ziyarar don nuna damuwarsa.

“Fafaroma Leo ya maimaita cewa lokaci ya yi da za a dakatar da wannan kisan kiyashi, cewa abin da ya faru ba zai yuwu ba, kuma dole ne mu tabbatar da cewa babu karin wadanda za su rasa rayukansu,” in ji Pizzaballa ga Vatican News.

Fafaroma ya bayyana “kusancinsa, kulawa, addu’a, goyon baya, da kuma burinsa na yin duk mai yiwuwa don cim ma ba kawai tsagaita wuta ba, har ma da kawo karshen wannan masifa,” ya kara da cewa.

Ziyarar ta zo ne kwana guda bayan wani harsashin tankin Isra'ila ya buga cocin, inda ya kashe mutum uku kuma ya jikkata wasu goma, ciki har da limamin cocin, Father Gabriel Romanelli.

‘Hadin kai da addu’o’i’

Cocin Holy Family ya kasance yana ba da mafaka ga kimanin fararen hula 600, ciki har da yara masu bukatun musamman.

Pizzaballa ya gode wa fafaroma saboda “hadin kai da addu’o’in da ya riga ya tabbatar mana da su,” yana mai cewa dukkan al’ummar Katolika a Gaza suna godiya.

Ya ce tawagar hadin kai ta kawo daruruwan ton na tallafin jinƙai, ciki har da abinci da kayan magani, tare da taimakawa wajen kwashe wadanda suka jikkata don jinya a wajen Gaza.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa daban, shugabannin cocin da shugabannin addinai a Birnin Ƙudus sun yi Allah wadai da harin Isra'ila.

“A cikin hadin kai mai karfi, muna yin Allah wadai da wannan laifi,” suka ce.

“Wuraren ibada wurare ne masu tsarki da ya kamata a kiyaye su. Haka kuma suna da kariya a karkashin dokar kasa da kasa. Kai hari kan coci da ke dauke da kimanin 'yan gudun hijira 600, ciki har da yara masu bukatun musamman, ya saba wa wadannan dokoki.

“Haka kuma cin zarafi da cin mutunci ne, sannan take hakkin rayuwar dan’adam, da kuma wulakanta wurin ibada mai tsarki ne.”

Sun yi kira ga al’ummar duniya da su matsa lamba don samun tsagaita wuta nan take, tabbatar da kariya ga duk wuraren addini da jinƙai, da kuma samar da agajin gaggawa ga fararen hula a fadin Gaza.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#