Darajar Bitcoin ta kai $71,000 a karon farko a yayin da masu zuba-jari suke sa rai baitul malin Amurka zai rage kuɗin-ruwa sannan gwamnatin ƙasar da ma ta Birtaniya za su ɗauki matakin da zai yi wa kasuwar kirifto daɗi
Darajar kuɗin kirifto na Bitcoin ta yi ƙaruwar da ba ta taɓa yi ba inda a ranar Litinin kowanne ɗaya ya kai $71,000 sakamakon ƙarin masu buƙatar kuɗin a daidai lokacin da Baitulmalin Amurka yake shirin rage kuɗin-ruwa na wannan shekarar.
An riƙa sayar da kowanne Bitcoin a kan $71,432 a kasuwar hada-hadar kuɗi ta yankin Asiya, a cewar alƙaluman da Bloomberg ta fitar, abin da ke nufin ya tashi da fiye da kashi 70 cikin ɗari a wannan shekarar.
Hakan na faruwa ne a yayin da aka samu labari cewa Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin kuɗi ta Birtaiya ta ce za ta bari a ƙirƙiro takardun lamuni da ke da alaƙa da kuɗaden kirifto.
Ta ɗauki matakin ne bayan a wannan shekarar hukumomi a Amurka sun nuna amincewarsu kan amfani da hannayen-jari da ke da alaƙa da kuɗaɗen kirifto na Bitcoin, abin da ya sa manyan masu zuba hannun-jari suka rungume shi.
