Sport
Dollar
41,4556
0.14 %Euro
48,7017
-0.54 %Gram Gold
4.955,0200
-1.09 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%An fara gangamin wayar da kan ne a kasuwar baje-koli ta kasa da kasa da ke Abuja, inda jami’an CBN suka jaddada bukatar ‘yan Nijeriya su rika mutunta darajar Naira.
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaddamar da wani gangamin wayar da kan jama'a a fadin kasar domin yaƙar wulaƙanta Naira, inda ya yi gargadin cewa masu karya doka za su iya fuskantar ɗaurin watanni shida a gidan yari ko kuma tarar da ta kai Naira 50,000 a karkashin dokokin da ake da su.
An fara gangamin wayar da kan ne a kasuwar baje-koli ta kasa da kasa da ke Abuja, inda jami’an CBN suka jaddada bukatar ‘yan Nijeriya su rika mutunta darajar Naira, kamar yadda gidan talabijin na ƙasa, NTA ya rawaito.
Babban Bankin ya damu da yawaitar ayyukan wulaƙanta naira kamar liƙin kudi a wurin bukukuwa, rubutu a kan kudi, ko yaga su yayin hada-hadar yau da kullum.
A cewar CBN, irin wannan dabi’a na zubar da mutuncin kudin kasa, yana kuma rage tsawon lokacin kudaden da ake kashewa, da kuma asarar biliyoyin nairori a duk shekara wajen bugawa da kuma maye gurbinsu.
“Mutunta Naira ba wai kawai a adana kudi ba ne, a’a yana kare tattalin arzikinmu da kuma martabar kasa,” in ji wani jami’in CBN a yayin kaddamarwar.
"Kowane aikin wulaƙanci yana aika saƙo mara kyau game da matsayinmu na mutane."
Sakamakon Shari'a
A wani ƙarin bayani da CBN ya yi a shafinsa na intanet kan kare darajar naira, ya ce a karkashin sashe na 21 na dokar CBN ta 2007, wulaƙanta Naira laifi ne da za a hukunta mutum saboda shi.
Masu laifin na iya fuskantar:
Ɗaurin wata shida a matsayin mafi ƙarancin lokacin da mutum zai yi a gidan yari
Biyan tarar aƙalla naira 50,000,
Ko kuma duka biyun, ya danganta da tsananin laifin.
Laifukan sun haɗa da:
Liƙawa ko yin rawa a kan naira ko taka ta
Sayar da sababbin kuɗi a farashin da ya fi na tsofaffi
Yin rubutu a kan kuɗi ko yaga naira
Liƙe naira ko gutsire ta.
Hanyoyin darajta Naira da CBN ta fitar
Don taimakawa wajen daƙile wulaƙanta Naira, CBN na kira ga ‘yan kasa da su rungumi dabi’ar mutunta kudi.
Bankin ya fitar da ƙayyadaddun ƙa'idoji don inganta inganci da daɗewa ana amfani da kuɗi:
Kar ku liƙa Naira: Gara ku sa a ambulan idan kyauta za ku bayar ko ku yi taransufa
Kar ku yi rubutu a kan naira: Hakan na saka ta saurin tsufa
Ku guji duƙunƙuna naira ko liƙe ta. Ku dinga barinta kullum a miƙe a tsaftace
Ku daina bari ruwa ko maiƙo na taɓa ta
Ku dinga adana ta da kyau ta hanyar sakawa a walet ko jaka
Ƙarfafa tura kuɗi ta banki
A wani bangare na kamfe ɗin, CBN na kuma karfafa gwiwar ‘yan Nijeriya da su dinga amfani da hanyoyin tura kudi —kamar banki ta wayar hannu, ko ta intanet, ko POS, ko biya da kati—domin rage yadda ake wulaƙanta kudi da kuma inganta tsarin kudi mai tsafta.
Fitowa gangamin wayar da kai a ƙasa
Bayan kaddamarwar a Abuja, za a fadada gangamin wayar da kan zuwa wasu jihohi, kasuwanni, da kuma wuraren taron jama'a a fadin kasar.
CBN ya ce manufarsa ita ce sanya sauyin ɗabi’u kan yadda ‘yan Nijeriya ke tafiyar da kudadensu — suna daukar Naira ba wai kawai a matsayin wata doka ba har ma a matsayin wata alama ta alfahari da kasa.
"Mu daure mu kare kudadenmu. Mu kare darajarmu," CBN ya bukaci.
Comments
No comments Yet
Comment