Dollar

43,4800

-0.04 %

Euro

51,2902

-0.61 %

Gram Gold

6.577,2800

-3.12 %

Quarter Gold

11.661,9400

-2.17 %

Silver

113,2000

-2.83 %

Masu gabatar da karar sun ce hare-haren sun rusa gidaje da dama tare da haifar da asarar rayuka mai yawa a Yelwata da ke gundumar Guma ta jihar Benue.

An gurfanar da mutum 9 a kotu bisa zargin kisan mutum 150 a Yelwata na jihar Benue a 2025

A ranar Litinin ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a Nijeriya ta ba da umarnin a tsare wasu mutum tara da ake zargi da laifin ta'addanci, sakamakon zargin su da kai hari kan al'ummar Yelwata da ke jihar Benue a ranar 13 ga Yuni, 2025, inda aka yi wa kimanin mutane 150 kisan kiyashi.

Jihar Benue da ke yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya ya yi kaurin suna wajen rikice-rikice a ƙasar. Sannan yankin ya kwashe shekaru da dama yana fuskantar tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya da kuma na kabilanci, lamarin da hukumomi suka kasa dakilewa gaba ɗaya.

Tuhume-tuhumen da aka shigar a babbar kotun, sun bayyana cewa waɗanda ake ƙara sun gudanar da tarurruka da suka tsara da kuma tara kuɗade da sayen makamai, sannan sun hada kan wasu ‘yan bindiga daga jihohi da dama kafin harin na ranar 13 ga watan Yuni, ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni da aka taba kai wa karkara a cikin shekaru masu yawa.

Kotun ta bayyana cewa shugaban 'yan bindigar, Ardo Lawal Mohammed Dono, ya hadu da wasu a jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Benue don tara kudi, da ba da umarni da kuma daukar mayaka.

Kazalika ana tuhumar da dama daga cikin mutanen ake zargi da samar da bindigogin kirar AK-47, da taimaka wa maharan, ko kuma samar musu da wurare masu aminci don shirya kai hare-hare.

Masu gabatar da karar sun ce hare-haren sun rushe gidaje da dama tare da haifar da asarar rayuka mai yawa a Yelwata da ke gundumar Guma ta jihar Benue.

Nijeriya na fuskantar matsin lamba kan tsaro tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya zargi ƙasar da gaza kare Kiristoci.

Sojojin Amurka sun kai hari kan wuraren da suka kira mabuyar 'yan ta'adda a ranar 25 ga Disamba. Hukumomin Nijeriya sun ce suna hada kai da Washington don inganta tsaro.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#