Sport
Dollar
43,4990
0.19 %Euro
51,6240
-0.9 %Gram Gold
6.788,9600
-9.85 %Quarter Gold
12.225,8700
-6.97 %Silver
116,5000
-28.39 %A cikin wata sanarwar manema labarai, jami’an watsa labarai na rundundar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce bayanan sirri sun tabbatar da kisan Julaibib, wani babban kwamandan ISWAP da ke aiki a yankin Gujba na abin da ake kira Timbuktu Triangle.
Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke Arewa Maso Gabashin Nijeriya, sun samu manyan nasarorin a fadin yankin, inda suka kashe manyan jagororin ‘yan ta’adda, suka tarwatsa tare da daƙile aikata laifuka ta hanyar ci gaba da ayyuka masu dogaro da bayanan leƙen asiri.
A cikin wata sanarwar, jami’in watsa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce bayanan sirri sun tabbatar da kisan Julaibib, wani babban kwamandan ISWAP da ke aiki a yankin Gujba na abin da ake kira Timbuktu Triangle.
A cewarsa, an kashe shugaban ‘yan ta’addan ne yayin wani artabu a kusa da Kimba, a Ƙaramar Hukumar Damboa ta Jihar Borno, a ranar 30 ga Janairun 2026.
Uba ya kara da cewa wasu bayanan sirri sun nuna cewa kawar da wannan kwamanda ya jefa ‘yan ISWAP da ke yankin cikin ruɗani, inda rahotanni ke nuna cewa an kashe wasu da dama daga cikin mayakan su a yayin aikin.
“Wannan muhimmin ci gaba babbar barazana ce ga tsarin jagoranci da sarrafa ayyuka na ISWAP a yankin,” in ji sanarwar.
A wani lamari mai alaƙa da haka, Uba ya bayyana cewa sojojin Operation Hadin Kai, tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF), sun kashe ‘yan ta’adda uku a yayin wani kwanton-ɓauna da aka shirya tsakanin garuruwan Ngazalgana da Lamusheri a Jihar Borno.
Ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri game da motsin ‘yan ta’addan a yankin.
“Sojoji sun shirya kwanton-ɓauna cikin dabara a kan hanyar da aka gano, suka yi wa ‘yan ta’addan luguden wuta mai ƙarfi, wanda ya kai ga kashe ‘yan ta’addan uku, yayin da wasu suka tsere ɗauke da raunukan harbi. An kwato bindigogin AK-47 biyu daga wurin,” in ji shi.
A cewarsa, wannan aiki na daga cikin kokarin da ake ci gaba da yi domin hana ‘yan ta’adda ‘yancin motsi tare da raunana karfin ayyukansu a dukkan yankin.
Comments
No comments Yet
Comment