Ronaldo ne dan wasa daya tilo da ya ci bugun fenariti dinsa cikin duka bugun da ’yan wasan Al-Nassr suka buga.

An cire ƙungiyar Al Nassr ta su Ronaldo daga Gasar Asian Champions League

Ƙungiyar Al-Ain ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta fitar da ƙungiyar Al Nassr wacce Cristiano Ronaldo ke wasa daga Gasar ƙungiyoyin nahiyar Asiya wato Asian Champions Leaguea a bugun fenariti da ci 3-1.

Al-Nassr ce ta fara yin rashin nasara a wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga da ci 1-0, sai dai Al-Nassr ta yi rashin nasara a gida a wasan da suka a jiya Litinin, inda aka tashi wasan 4-3, kafin daga bisani bugun fenariti ya raba-gardama a tsakaninsu.

Ronaldo ya barar da wata babbar dama da ya samu yayin wasan, ko dayake ya yi nasarar cin bugun fanareti a minti na 118, abin da ya sa jumullar sakamakon wasannin biyu ya koma 4-4.

Ronaldo ne ɗan wasa ɗaya tilo da ya ci bugun fenariti ɗinsa cikin duka bugun da ƴan wasan Al-Nassr suka buga.

Sai dai a minti na 72 tsohon wasan Manchester United Alex Telles ya ci kwallo da ta tilasta aka tafi karin lokaci bayan cikar minti 90, sannan an kori dan wasan Al Nassr Ayman Yahya bayan ya samu jan kati.

Yanzu kungiyar Al-Ain za ta san kungiyar da za ta fafata da ita a mataki na gaba na gasar a kwanakin da ke tafe.

#