A karon farko a kasar Nijar, an bude wata makarantar da za ta horar da yara kwallon kafa, mai suna Fenifoot Academy.
A kokarin ci gaba da habaka harkar wasanni a kasar Nijar, an samar da wata makaranta da za ta mayar da hankali kan horar da yara kwallon kafa, don zama kwararru.
A tashin farko, makarantar, wadda ke Yamai babban birnin kasar, za ta fara horar da yara 60, da suka hada da yara 30 'yan kasa da shekara 13, da kuma yara 30 'yan kasa da shekara 15, a cewar Silimane Mohamed, sakataren hukumar ta Fédération Nigérienne De Football.
Sakataren hukumar Kwallon Kafar ta Nijar, ya kara da cewa wannan cibiyar ba wai kwallo kafa kadai za ta koyar da yaran ba, saboda daga cikin yaran akwai 'yan makaranta da wadanda ba sa makaranta.
Sakamakon haka, wadanda ba sa makaranta akwai wani sashen da aka ware domin koya musu ayyukan hannu.
Ya kara da cewa hukumar kwallon kafar za ta yi bakin kokari domin ganin ta farfado da kimar wasannin kwallon kafa a Nijar.
A tarihin dai, kasar ta Nijar ta taba halartar gasar cin kofin kasashen Afrika a shekarar 2011 da 2012. Sai dai tun a karawar rukuni aka fitar da ita daga gasar.
