Dollar

43,0410

0.04 %

Euro

50,3431

-0.29 %

Gram Gold

6.210,7800

1.04 %

Quarter Gold

10.390,9600

0.51 %

Silver

112,1800

6.44 %

A yanzu Amurka za ta yanke shawara kan makomar Venezuela bayan "kama" Maduro", a cewar Shugaba Trump, yana mai ƙarawa da cewa "za mu shiga cikin samar da sabon shugaba sosai."

Amurka ba za ta bari kowa ya ci gaba daga inda Maduro ya tsaya ba - Trump

Amurka yanzu tana yanke shawara kan abin da zai biyo baya ga Venezuela bayan "kama" Shugaban ƙasa Nicolas Maduro da matarsa Cilia Adela Flores, in ji Shugaban Amurka Donald Trump, yana mai ƙarawa da cewa Washington "za ta shiga cikin sa sosai".

"Za mu shiga cikin sa sosai. Kuma muna son samar da 'yanci ga mutane," kamar yadda Trump ya gaya wa Fox News a wata hira ta waya ranar Asabar, yana mai ƙarawa da cewa wannan gagarumin hari na rundunar soji na musamman na Amurka ya nuna cewa "ba za a rinjayi washington ba."

Trump ya ƙara da cewa Amurka za ta sa “hannu dumu-dumu” a ɓangaren man fetur ɗin Venezuela.

"Muna da kamfanonin mai mafiya ƙarfi a duniya, mafiya girma, mafiya kyau, kuma za mu shiga sosai cikin harkar," in ji shi.

Trump ya ce Maduro da matarsa suna wani jirgin ruwa na yaƙki na Amurka kuma za su fuskanci gurfanarwa a New York.

Ya ce an kama Maduro a wani wuri da ake gadinsa sosai, kuma ya ƙara da cewa babu Amurkawa da aka kashe a harin na soji na ranar Asabar.

"Yana cikin wani wuri da ake gadinsa sosai," in ji Trump. "Ku sani, abin mamaki ne cewa babu wanda muka rasa," kamar yadda ya faɗa, yana ƙarawa da cewa "wasu sun ɗan ji rauni, amma sun dawo kuma ana sa ran za su kasance cikin koshin lafiya."

"Na kalli komai, da gaske, kamar ina kallon shirin talabijin." kamar yadda Trump ɗin ya bayyana.

"Mun kalli kowane ɓangare na aikin."

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#