Sport
Dollar
43,0463
0 %Euro
50,3136
-0.01 %Gram Gold
6.160,9800
-0.9 %Quarter Gold
10.399,3200
0.08 %Silver
108,4000
-3.62 %An kama kifin nau’in bluefina tuna mai nauyin kilogiram 243 ne a gaɓar tekun Oma a arewa maso gabashin Japan, kuma wani kamfani Kiyomura Corp da ke cikin rukunin kantunan sayar abinci na Sushizanmai ne ya saye shi.
An sayar da wani kifi a kan kudi har dala miliyan 3.2 (kwatankwacin Naira biliyan 4.5) a wajen gwanjon farko da aka yi a kasuwar kifaye ta Toyosu a birnin Tokyo na Japan ranar Litinin.
An kama kifin nau’in bluefina tuna mai nauyin kilogiram 243 ne a gaɓar tekun Oma a arewa maso gabashin Japan, kuma wani kamfani Kiyomura Corp da ke cikin rukunin kantunan sayar abinci na Sushizanmai ne ya saye shi.
“Tuna na farko a shekarar nan ya zo mana da sa’a. Muna fatan mutane da dama za su ji daɗin cin kifin har ya ƙara musu karsashi,” in ji Shugaban Kamfanin Kiyomura, Kiyoshi Kimura, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kyodo ya rawaito.
Za a yayyanka kifin ne a wani reshen kantin abinci na Sushizanmai da ke Tsukiji sai a aika shi sauran rassan kantin da ke faɗin ƙasar. Duk da tsadar yadda aka sayi kifin, kamfanin ya yi alkawarin sayar wa mutane a kan farashin da suka saba saya.
A cewar hukumar kula da birnin Tokyo, wannan farashi shi ne mafi tsada da aka taɓa sayen kifi tun daga shekarar 1999 da aka fara samun bayanan farashin gwanjon kifaye.
A wajen gwanjon, an gabatar da nau’ukan kifin tuna sosai, lamarin da ya sanya karsashi ga masu saye da masu sayarwa.
Kazalika ya ja hankalin masu yawon buɗe ido ‘yan ƙasashen waje da suka halarci wajen don shaida taron da aka saba yi duk shekara.
Masu saye sukan kashe makuɗan kuɗi a wajen gwanjon farko na shekara, saboda an yi amannar cewa hakan yana kawo sa’a ga masu kantunan sayar da abinci wajen samun kasuwa.
Comments
No comments Yet
Comment