Dollar

43,0559

0.03 %

Euro

50,2767

-0.09 %

Gram Gold

6.175,9200

0.27 %

Quarter Gold

10.302,3900

-0.93 %

Silver

105,5800

-2.56 %

Zan-zangar matsin tattalin arziki a Iran ta janyo hankulan kasashen duniya, ciki har da shugabannin kasashe abokan hamayya, Isra’ila da Amurka, wanda ya tilasta wa sojoji mayar da martani.

Shugaban Rundunar Sojin Iran ya yi barazanar mayar da martani ga Trump da Netanyahu

Babban hafsan sojin Iran ya yi gargadin cewa kasar ba za ta tsaya ta tana kallo a yi mata barazana daga ƙasashen waje ba, bayan da Amurka da Isra'ila suka goyi bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar.

"Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ɗauki ƙaruwar kalaman batanci ga al'ummar Iran a matsayin barazana kuma ba za ta lamunci ci gaba da hakan ba tare da mayar da martani ba," in ji Janar Amir Hatami, a cewar kamfanin dillancin labarai na Fars.

Hatami, kwamandan sojojin Iran ya yi gargaɗin cewa "idan maƙiya suka yi kuskure," martanin Iran zai fi ƙarfi fiye da lokacin yaƙin kwanaki 12 da Isra'ila na watan Yunin da ya gabata.

A cikin 'yan kwanakin nan, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shiga tsakani a Iran idan aka kashe masu zanga-zanga, yayin da Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya nuna goyon baya ga zanga-zangar.

A ranar 28 ga Disamba, 'yan kasuwa a Tehran sun gudanar da zanga-zanga kan hauhawar farashi da rugujewar kudin kasar rial, wanda ya haifar da daukar irin wannan mataki a birane da dama.

Zanga-zangar ba ta kai matsayin zanga-zangar 2022 zuwa 2023 ba, ballantana zanga-zangar da aka yi a titunan kasar a shekarar 2009 bayan zaben shugaban kasa.

Amma zanga-zangar tattalin arziki ta jawo hankalin kasashen duniya, ciki har da shugabannin kasashen da ke adawa da Iran.

"Muna kallon ta sosai. Idan suka fara kashe mutane kamar yadda suka yi a baya, ina ganin Amurka za ta far musu da karfi," in ji Trump ga manema labarai a ranar Lahadi.

A halin yanzu, Netanyahu ya shaida wa majalisar ministocin Isra'ila cewa "Muna goyon bayan gwagwarmayar al'umar Iran da kuma burinsu na samun 'yanci da adalci."

A ranar Litinin, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta zargi Trump da Netanyahu da tayar da hankali da kuma kokarin kawo cikas ga hadin kan kasar Iran.

Yakin da aka yi a watan Yuni ya fara ne da harin da Isra'ila ta kai wa sojojin Iran da cibiyoyin nukiliyarta.

Amurka ta shiga cikin hare-haren na dan lokaci, inda ta kai hari kan manyan wuraren nukiliya na Iran guda uku.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#