Dollar

43,0387

0.02 %

Euro

50,3196

-0.03 %

Gram Gold

6.171,2600

-0.74 %

Quarter Gold

10.399,3200

0.08 %

Silver

108,5400

-3.5 %

An yin garkuwa da babban jami'in mai ritaya a safiyar ranar 5 ga Janairun 2026 da misalin ƙarfe 00:45 daga gidansa da ke daura da Cocin Salvation Army da ke kan titin Rukuba, karamar hukumar Bassa.

Dakarun Nijeriya sun kubutar da wani Kanal mai ritaya da aka yi garkuwa da shi a jihar Filato

Dakarun Sojin Nijeriya da ke kai Farmakan ‘Enduring Peace’ sun kubutar da wani babban jami’in soji, Kanal Ajanaku mai ritaya, bayan garkuwa da shi da wasu ‘yan bindiga suka yi a yankin Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

An yin garkuwa da babban jami'in mai ritaya a safiyar ranar 5 ga Janairun 2026 da misalin ƙarfe 00:45 daga gidansa da ke daura da Cocin Salvation Army da ke kan titin Rukuba, karamar hukumar Bassa.

Bayan samun kiran gaggawa, sojojin Sashe na 1 da na 3, da ke kai Farmakan ‘ENDURING PEACE’ sun yi gaggawar fita tare da tare da bin diddigin inda suka nufa a hanyar filin shakatawa na Wildlife Park.

Sojojin, tare da hadin gwiwar Sashen Leken Asiri na Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, da kuma 'yan banga na yankin, sun ci gaba da gudanar da bincike da ceto mai zurfi, suna farautar maboyar masu laifi a cikin kogo da tsaunukan duwatsu da ke yankin.

Daga baya a wannan ranar, da misalin ƙarfe 14:00, masu garkuwar sun tuntubi matar jami'in mai ritaya da aka yi garkuwa da shi, kuma suka nemi a biya su fansar Naira Miliyan Ɗari Biyu (₦200,000,000.00).

Bayan sun lura da yawan kasancewar sojoji da matsin lamba daga sojojin, masu garkuwar sun yi barazanar kashe wanda suka yi garkuwan da shi idan ba a dakatar da ayyukan bincike ba.

Saboda haka, sojoji suka koma gudanar da ayyukansu a ɓoye, wanda ya kai ga nasarar ceto Kanal Ajanaku mai ritaya da misalin ƙarfe 17:30 a ranar 5 ga Janairun 2026 a gefen Rafiki Axis, ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato, ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

A yanzu ana ci gaba da duba lafiyar jami’in sojan da aka kubutar kuma yana cikin yanayi mai kyau, a cewar rundunar sojin ƙasar. Ta kuma ce daga baya zai bayar da bayanan yadda za a kamo ‘yan ta’addar da suka gudu.

A halin yanzu, sojojin na ci gaba da kai hare-hare a cikin dazuzzukan da ke kewaye don kama masu garkuwa da mutanen da suka gudu da kuma wargaza hanyoyin sadarwarsu yayin aikata laifuka.

Rundunar Sojojin Najeriya, ta hanyar Farmakan ‘ENDURING PEACE’, ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi kuma za ta ci gaba da hana masu aikata laifuka 'yancin yin aiki a duk fadin yankin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#