Dollar

40,6884

0.05 %

Euro

47,5718

0.22 %

Gram Gold

4.419,3700

0.37 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bayanan shekarar 2025 na hukumar NEMA sun nuna cewa ambaliyar ruwan ta fi shafar yara da mata.

Ambaliyar shekarar 2025: Mutum 191 sun mutu, 94 sun ɓata a Nijeriya – NEMA

Alƙaluma daga hukumar ba da agajin gaggawa ta tarayyar Nijeriya sun nuna cewa mutum 191 sun mutu kuma 94 sun ɓata  yayin ambaliya ta shafi mutum 134,435 a bana kawo yanzu.

Hukumar ta bayyana cewa mutum 239 sun jikkata a mataki daban daban, inda ambaliya ta raba mutum 48,056 da gidajensu kuma ta shafi gidaje 9,499 da gonaki 9,450 a cikin ƙananan hukumomi 47 a jihohin 20.

Bayanan shekarar 2025 na hukumar NEMA sun nuna cewa ambaliyar ruwan ta fi shafar yara da mata.
Alƙaluman na cewa: “kawo yanzu a ambaliyar bana ta shafi yara 60,071 da mata 41,539 da maza 27,121 da manya 5,704 da kuma masu buƙata ta musamman”.

Jihohin da suka fi yawan waɗanda da lamarin ya shafa sun haɗa da Jihar Imo inda ta shafi mutum 28,030 da Jihar  Ribas inda ta shafi mutum 22,345 da Jihar Adamawa inda ta shafi mutum 12,613 da jihar Abia inda ta shafi mutum 11,907 da Jihar Borno inda ta shafi mutum 8,164 da kuma Jihar Kaduna inda ta shafi mutum 7,334.

Jihohi 20 da lamarin ya shafa su ne Abia da Birnin Tarayya da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bayelsa da Borno da Delta da Edo da Gombe da Imo da Jigawa da Kaduna da Kano da Kogi da Kwara da Neja da Ondo da Ribas da kuma Jihar Sokoto. 

Hukumar ta ce ababen da waɗanda lamarin ya shafa suka fi buƙata su ne: abinci da muhalli da abinci mai gina jiki da ruwa da tsabta da kiwon lafiya da ilimi da tsaro.

Babban ƙalubalen da aka gano bayan amabliyar in ji hukumar NEMA sun haɗa da ƙarancin kayayyaki da rashin damar shiga yankunan da lamari ya faru da barazanar rashin tsaro da adawa daga al’umma da kuma raunin gudanarwa. 

A shekarar 2024, kimanin mutum miliyan 5 ne lamarin ya shafa inda ambaliyar ta raba mutane miliyan 1.2 da gidajensu sannan mutane 16,000 suka jikkata.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#