Sport
Dollar
40,6935
0.06 %Euro
47,1814
0.06 %Gram Gold
4.413,6900
0.06 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tsuntsayen masu rai fiye da 1,620 sun haɗa da nau'ukan kanari da aku da sauran su.
Jami’an Hukumar Kwastam ta Nijeriya a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke jihar Legas sun ƙwace wasu tarin tsuntsayen da aka yi niyyar fitarwa zuwa Kuwait ba bisa ƙa’ida ba.
Tsuntsayen masu rai fiye da 1,620 sun haɗa da nau'ukan kanari da aku da sauran su.
An yi wannan kamu ne a karkashin jagorancin Shugaban Hukumar ta Kwastam na filin jirgin saman, Michael Awe, sakamakon binciken da jami’an ‘yan sintiri na wajen suka yi.
Awe ya ce a matsayin Nijeriya na ƙasar da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayyar kasa da kasa kan namun daji da tsuntsaye, babu wata jigilar dabbobi da za a yi ba bisa ƙa'ida ba ta iyakokin ƙasar ba tare da izini ko takardun da ake bukata ba.
Ya bayyana cewa, an fara gudanar da bincike domin kamo wadanda suke da hannu a wannan aika-aika, yayin da aka miƙa tsuntsayen domin mayar da su inda ya kamata su dinga rayuwa.
Awe ya ce "Ba zan taɓa bari a ƙarƙashin mulkina a yi wata jigila irin wannan ba bisa ƙa'ida ba ta wannan filin jirgin sama. Jami'anmu na cikin shirin ko-ta-kwana. Suna sa ido don ganowa da kuma daƙile duk wani abu da ya saɓa wa doka," in ji Awe.
Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta ce a matsayinta na mai rattaba hannu kan yarjejeniyar CITES, ƙasar ta himmatu wajen hana fataucin namun daji ba bisa ƙa'ida ba, tare da tabbatar da cewa an daidaita kasuwancin ƙasa da ƙasa na nau'ukan dabbobin da ke cikin hatsari, da kuma tabbatar da ɗorewar hakan.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don ganowa da kuma damke wadanda ke da hannu a yunkurin fasa-kwaurin, za a mika wa hukumar kula da gandun daji ta kasa (NPS) tsnutsaye don mayar da su cikin muhallinsu.
Comments
No comments Yet
Comment