Dollar

40,7015

0.02 %

Euro

47,2204

1.43 %

Gram Gold

4.394,9300

2.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan 'yan bindigan a Zamfara da ke arewacin Nijeriya sun kashe mutum 33 da suka yi garkuwa da su tun a watan Fabrairu duk da samun kuɗin fansa na naira miliyan 50 da suka yi.

'Yan bindiga sun sace fiye da mutum 50 a Jihar Zamfara

Wasu 'yan bindiga sun sace fiye da mutum 50 a arewa maso yammacin Nijeriya a wani gagarumin hari da ‘yan garkuwar suka kai, kamar yadda wani rahoton sa ido kan rikici da aka shirya ga Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, wanda AFP ta gani a ranar Lahadi.

Rahoton ya ce, 'yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Sabon Garin Damri da ke jihar Zamfara a ranar Juma'a.

Waɗannan ƙungiyoyin 'yan bindiga galibi suna yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, inda suke ƙwace dukiyoyin jama’ar ƙauye, kuma suna tilasta musu biyan haraji.

Rahoton ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan gagarumar satar mutane a yankin Ƙaramar Hukumar Bakura a wannan shekarar, yana mai nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar irin waɗannan hare-hare a Jihar Zamfara, musamman a arewacin jihar.

‘Yan bindiga sun kashe mutane 33 duk da samun kudin fansa

Matsalar 'yan bindiga a Nijeriya ta samo asali ne daga rikici kan filaye da wuraren ruwa tsakanin makiyaya da manoma, amma yanzu ta rikiɗe zuwa wani nau'in laifukan da ake shiryawa kafin aikatawa, inda ƙungiyoyin ‘yan bindiga ke cin zarafin al'ummomin karkara.

Hare-haren sun tilasta wa mutane barin gonakinsu.

A watan da ya gabata, 'yan bindiga a Zamfara sun kashe mutum 33 da suka yi garkuwa da su tun watan Fabrairu duk da samun kuɗin fansa na naira miliyan 50, yayin da jarirai uku suka mutu a tsare, kamar yadda jami'ai da mazauna yankin suka bayyana.

Makonni biyu da suka gabata, sojojin Nijeriya sun kashe aƙalla mambobi 95 na wata ƙungiyar 'yan bindiga a wata musayar wuta da hare-haren sama a Jihar Neja da ke arewa maso yamma.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#