Sport
Dollar
40,7015
0.02 %Euro
47,2204
1.43 %Gram Gold
4.394,9300
2.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wata sanarwa da ƙungiyar National Association of Nigeria Nurses and Midwives ta fitar ta ce gwamnati ta saurari ƙorafinsu kuma ta faɗi "lokacin" da za ta cika alƙawuran da ta ɗauka, sai dai ta ce za ta sanya ido sosai don ganin ko za ta ɗauki mataki
Ma’aikatan jinya na asibitocin gwamnatin Nijeriya ranar Asabar sun dakatar da “yajin aikin gargaɗi” na kwana bakwai da suka soma bayan sun cim ma yarjejeniya da hukumomin ƙasar waɗanda suka yi alƙawarin biyan buƙatunsu.
Wata sanarwa da ƙungiyar National Association of Nigeria Nurses and Midwives ta fitar ta ce gwamnati ta saurari ƙorafe-ƙorafensu kuma ta bayyana "lokacin" da za ta cika alƙawuran da ta ɗauka, sai dai ƙungiyar ta ce za ta sanya ido sosai don ganin ko za a cika alƙawuran.
Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki ne ranar Laraba 30 ga watan Yuli, inda suka yi barazanar mayar da shi yajin aiki na dindindin muddin gwamnatin ba ta aiwatar da buƙatunsa ba cikin kwana bakwai.
Sun buƙaci a ƙara musu albashi da samar da ƙarin ma’aikata a fannin jinya da kuma kyautata yanayin aikinsu.
Ƙungiyar ma’aikatan jinyar ranar Juma’a ta gana da Ministan Kiwon Lafiya da Walwala na Nijeriya Farfesa Ali Pate da takwaransa aikinsa na Ƙwadago da Samar da Ayyuka, Muhammad Dingyadi.
Tun da farko Farfesa Pate ya sanar da cewa ma’aikatan jinyar sun janye yajin aikin bayan ganawar tasu, sannan ya sha alwashin cewa gwamnati za ta ɗauki mataki kan ƙorafe-ƙorafen da suka gabatar mata.
Kazalika a ganawar an amince cewa ba za a hukunta duk wani ma’aikacin jinya da ya shiga yajin aikin ba.
Comments
No comments Yet
Comment