Dollar

40,6786

0.07 %

Euro

47,1468

-0.04 %

Gram Gold

4.403,7300

0.19 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Hasashen na kwanaki uku da aka fitar a Abuja ranar Lahadi, na zuwa ne bayan ruwan sama ya lalata gidaje kimanin 50 da gonaki da wuraren ibada a Jihar Filato.

NiMet ta yi hasashen ruwan sama babu ƙaƙƙautawa na kwana uku a faɗin Nijeriya daga ranar Litinin

Hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da tsawa na kwaki uku a faɗin ƙasar daga ranar Litinin, lamarin da ke ƙara barazanar ambaliya a wasu jihohin ƙasar.

Hasashen na kwanaki uku da aka fitar a Abuja ranar Lahadi, na zuwa ne bayan ruwan sama ya lalata gidaje kimanin 50 da gonaki da wuraren ibada a Jihar Filato.

Hukumar ta yi hasashen cewa za a yi tsawa da ruwan sama a jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da Adamawa da Taraba da Sokoto da Kebbi da Zamfara da Jigawa da Kano da kuma  Katsina ranar Litinin, kuma lamarin zai yi ƙamari zuwa yammacin ranar.

Akwai yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba da kuma Bauchi a wannan lokacin da aka yi hasashen,” kamar yadda NiMet ta bayyana a sanarwar.

A tsakiyar Nijeriya, ana sa ran saukar ruwan sama kaɗan da safiya a jihohin Binuwai da Neja da Kogi da Nasarawa da Kuma Birnin Tarayya Abuja. Kuma zuwa rana da yamma, ana sa ran ruwan saman zai kai jihohin Filato da Kwara da kuma sauran jihohi maƙwabta.

A yawancin jihohin kudancin ƙasar dai hasashen hadari ake yi, inda ake ganin yiwuwar samun ruwan sama kaɗan a jihohin Ebonyi da Enugu da Imo da Anambra da Abia da Ogun da Edo da Delta da Legos da Ribas da Cross Rivers da Akwa Ibom da kuma Bayelsa da sanyina safiya. Amma daga baya  ana sa rai za a yi ruwa mai yawa, inda NiMet ke gargaɗin cewa za a iya samun ambaliya a jihohin Oyo da Ogun da Edo da kuma Delta.

Ranar Talata, hukumar tana hasashen cewa za a ci gaba da samun ruwan sama mai yawa da tsawa a yankin arewacin ƙasar musamman a jihohin Taraba da Katsina da Kebbi da Sokoto da Kaduna da kuma Zamfara. “Ana tsammanin matsakaicin ruwan sama da tsawa a faɗin yankin daga baya a ranar,” in ji hukumar.

Jihohin tsakiyar ƙasar ciki har da Abuja, na tsammanin ruwan sama mai ɗaukewa da dawowa, yayin da jihohin kudancin ƙasar daga Legas zuwa birnin Calabar za su iya fuskantar ruwan sama babu ƙaƙƙautawa.

NiMet ta ja hankalin mazauna jihohin Anambra da Delta da Bayelsa da Cross River da kuma Akwa Ibom su shirya wa yiwuwar ambaliya.

Zuwa ranar Laraba, ana sa ran ruwan sama da tsawa zai karaɗe jihohin Taraba da Kaduna cikin sanyin safiya, inda kuma za a samu guguwa da ruwan sama daga baya a jihohin Borno da Bauchi da Gombe da Jigawa da kuma Kano.

Yankin tsakiyar ƙasar kuma zai sake ganin yayyafi da safiya, kuma da rana za a yi ruwan sama mai yawa.

A kudanci kuwa ana hasashen za a yi ruwan sama mai ɗaukewa da dawowa a jihohin Legas da Ribas da Bayelsa da Cross River. Jihar Bayelsa ta fi fuskantar barazanar ambaliya a tsakiyar mako, in ji hukumar

Hukumar ta yi kira ga mazauna jihohin su ɗauki matakan kauce wa barazanar ambaliyar

“[Ku] kaurace wa tuƙi a cikin ruwan sama mai ƙarfi, kuma jihohin da ke da yiwuwar samun ambaliya su yi tsare-tsarensu na ba da agajin gaggawa nan-take,” in ji hasashen.

NiMet ta kuma shawarci magidanta su ɗaure ababen da ka iya faɗuwa kuma su sanya rigunan sanyi tare da cire kayan lataroni daga lantarki a lokacin guguwa.

Hukumar ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama su nemi shawarwari na yanayi wajen shirya jadawalin jigilar matafiyansu.

NiMet ta buƙaci ‘yan Nijeriya su bibiyi shafinta na intanet don samun ƙarin bayani kan yanayi.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#