Dollar

40,6783

0.07 %

Euro

47,1659

0.01 %

Gram Gold

4.416,0000

0.47 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Jami'an tsaron sun ce sun halaka 'yan ta'addan ne a wani samame na musamman da suka kai garin Bariire a yunƙurinsu na ƙwato garin

Jami'an tsaro a Somaliya sun kashe 'yan ta'addan Al Shabab fiye da 50

Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya (AUSSOM) ta bayyana cewa an kashe fiye da 'yan ta'adda 50 na Al Shabab a wani aikin soji na haɗin gwiwa da sojojin Somaliya a garin Bariire da ke yankin Lower Shabelle.

A yayin wannan aiki, an samu rahoton cewa da dama daga cikin 'yan ta'addan Al Shabab sun ji munanan raunuka, kamar yadda wata sanarwa daga kungiyar AUSSOM ta bayyana a ranar Lahadi.

"Sojojin AUSSOM da SNAF sun ƙuduri aniyar ƙwato garin Bariire da sauran yankunan da ke ƙarƙashin ikon Al Shabab domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa ga al'ummar Somaliya," in ji El Hadji Ibrahima Diene wanda shi ne wakili na musamman na Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka (SRCC) a Somaliya, a cikin sanarwar.

Haka kuma, ƙungiyar ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke cewa an samu asarar rayuka masu yawa daga ɓangaren sojojinta a wannan aiki.

Bariire wani muhimmin gari ne na noma da ke da tazarar kilomita 73 (mil 45) kudu maso yamma da babban birnin Mogadishu.

Al Shabab, wadda ta shafe fiye da shekaru 16 tana tayar da hankali a Somaliya, tana kai hare-hare akai-akai kan jami'an tsaro, ma'aikatan gwamnati da fararen hula.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#