Dollar

40,6788

0.08 %

Euro

47,1595

-0.03 %

Gram Gold

4.420,7600

0.58 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Nijeriya ta doke Mali wajen kafa tarihi na lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka a karo na biyar a jere ranar Lahadi.

D'Tigress ta Nijeriya ta shirya wa Kofin Mata Na Duniya bayan ta kafa tarihin lashe Gasar ta Afirka

‘Yan Nijeriya na murnar nasarar da tawagar matan ƙasar ta ƙwallon kwando, D'Tigress, ta yi wajen kafa tarihi ta hanyar lashe gasar ƙwando ta Afirka ta mata ta shekarar 2025, FIBA AfroBasket, a karo na biyar a jere.

‘Yan tawagar sun doke Mali da ci 78-64 a wasan ƙarshe ranar Lahadi a Palais des Sports Treichville a birnin Abidjan, na ƙasar Côte d'Ivoire.

Duk da cewa Mali na gabansu da ci 26-20 a ƙarshen hutun kwatan lokaci na farko, Nijeriya ta mamaye sauran kwatan lokaci ukun inda ta samu cikakkiyar nasara.

Shugaba Bola Tinubu ya taya tawagar murna.

‘‘Wasa mai kyawun gaske ya sa kuka zama zakarun Afirka a sau biyar a jere kuma sau bakwai jumulla. Sannu da aiki, Kociya Rena da tawaga. Kun ƙayatar da Nijeriya. Ina jiran dukkanku da kofin,’’ in ji Tinubu a shafinsa na X.

Wasan na ƙarshe an buga shi ne tamkar ana sake buga wasan ƙarshe na gasar shekarar 2021 lamarin da ya sake tayar da hamayyar da aka shafe shekara goma ana yi tsakanin tawagogin biyu.

Tun shekarar 2011, Nijeriya da Mali sun haɗu sau shida, inda kowace tawaga ta yi nasara sau uku. Tawagogin biyu sun nuna ƙwarewa da jajircewa a kan hanyarsu ta zuwa wasan ƙarshe.

Nijeriya ce ta yi nasarar zuwa ta ɗaya a rukunin D inda ta yi nasarori biyu, saboda nasarorin da ta yi kan tawagopgin Mozambique da Rwanda.

Sannan kuma suka yi kaca-kaca da Kamaru da ci  83-47 a wasan kusa da daf da na ƙarshe, inda suka nuna fin ƙarfinsu a filin wasa yayin da gasar ke daɗa nuna cigaban da ake samu a fagen ƙwallon kwando a Afirka. 

Wasan ƙarshen wannan gasar  ya kuma kasance tamkar maimaita wasan ƙarshe ne gasar shekarar 2021 inda Nijeriya ta yi nasara da ci 70-59.

‘Yan wasa takwas daga kowace tawagar da suka buga gasar ta 2021 na cikin waɗanda suka buga wasan ƙarshe na baya bayan nan.

Wannan shi ne karo na bakwai da Nijeriya ta lashe kofin gasar, kuma nasarar ta ba ta damar shiga gasar ƙwallon kwando ta mata ta duniya FIBA ta shekarar 2026 da za a yi a birnin Berlin, ta Jamus.

Mali da South Sudan da Senegal za su fafata a matakin neman cike gurbi ɗaya tilo shiga gasar cin kofin duniya ta ƙwallon kwando a matan da ya rage a watan Maris mai zuwa.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#