Dollar

40,7015

0.02 %

Euro

47,2204

1.43 %

Gram Gold

4.394,9300

2.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Komawar tauraron ɗan wasan ta biyo bayan tattaunawa da Napoli kan Osimhen, wanda a bara ya buga wa Galatasaray wasa a matsayin aro.

Osimhen ya kammala yarjejeniyar komawa Galatasaray daga Napoli

Ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya ta cim ma matsaya kan ɗaukar Victor Osimhen daga Napoli ta Italiya, inda ɗan wasan ya samu tarba daga dubban magoya bayan ƙungiyar.

Osimhen, wanda ɗan asalin Nijeriya ne ya isa filin jirgin sama na Atatürk a Istanbul a daren Laraba, tare da rakiyar Mataimakin Shugaban Galatasaray, Abdullah Kavukcu.

Galatasaray ta daɗe tana muradin ɗauko Osimhen a matsayin kyauta da a ce kwantiraginsa ta ƙare da Napoli, amma duk da haka ƙungiyar ta ƙure adaka don ganin ta kawo shi.

Da yake jawabi ga masoya, Osimhen ya ce, “Ban san kalmomin da zan yi amfani da su don bayyana yadda nake ji ba. Na ji daɗi sosai kasancewata a nan. Duba taron jama’ar nan, duba mutanen da suka bi jirgin.

“Na dawo gida. Nan ne inda nake so na kasance. Na ji daɗin kasancewa a nan, na dawo. Ina so in gode wa shugabanninmu, Abdullah Kavukcu da George Gardi da Okan Buruk da duk waɗanda suka taimaka wajen dawowata”.

Ɗan wasan mai shekaru 26 zai yi gwaje-gwajen lafiya ranar Alhamis, 31 ga Yuli. Bayan nan, zai sa hannu kan kwantiragi da Galatasaray ranar 2 ga Agusta, kamar yadda TRT Sport ta ruwaito.

‘Zakaran cin ƙwallo’

A bara tare da taimakon haziƙin ɗan wasan, Galatasaray ta ɗaga Kofin Trendyol Super Lig na Turkiyya, inda ɗan wasan ya ci kyautar wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a kakar.

Victor Osimhen ya zura ƙwallaye 37 tare da tallafin ƙwallaye 7 a wasanni 41 da ya buga wa tauraruwar ƙungiyar ta birnin Istanbul.

Baya ga Kofin Babbar Gasar Turkiyya, Galatasaray ce ta lashe kofin ƙalubale na ƙasar, wato Ziraat na Turkiyya bayan ta doke Trabzonspor da ci 3-0.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#