Sport
Dollar
40,5847
0.02 %Euro
46,6102
-0.6 %Gram Gold
4.299,5400
-0.94 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shirin na matakin share-fage ne, ƙarƙashin babban shirin Ƙwallon Ƙafa don Makarantu na FIFA, wanda aka zaɓi ƙasashen Nijar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya don yin gwaji.
Jamhuriyar Nijar da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, sun rattaba hannu kan takardar fahimtar juna game da shirin bunƙasa ƙwallon ƙafa a makarantu.
Wata sanarwa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijar ta FENIFOOT ta wallafa a shafinta na intanet a ƙarshen mako, ta ce an ƙulla wannan haɗin gwiwa ne ranar Asabar 27 ga Yulin 2025 a birnin Rabat na Morocco.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijar, ANP ne ya ambato sanarwar, inda ya ce shirin ya ƙunshi matakin share-fage ƙarƙashin babban shirin Ƙwallon Ƙafa don Makarantu na FIFA, wanda aka zaɓi ƙasashen Nijar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya don yin gwaji.
Taron ya gudana ne a hedkwatar ofishin yanki na FIFA da ke Rabat, wanda shi ma aka ƙaddamar da shi a ranar.
Mahalarta taron sun haɗa da shugaban FIFA Gianni Infantino, da shugaban hukumar FENIFOOT, Issaka Adamou, da mamban hukumar FIFA daga Nijar, Colonel-Major Djibrilla Hima Hamidou.
Darussan motsa-jiki
Akwai kuma mambobin gwamnatin Nijar, Dr. Elisabeth Shérif, Ministar Ilimi ta Ƙasa, da Mr. Sidi Mohamed Almahmoud, Ministan Matasa da Wasanni.
Shirin ya ƙunshi bunƙasa ilimi ta hanyar wasanni, inda ɓangarorin za su haɗa gwiwa don ƙarfafa ƙwallon ƙafa a makarantu, da amfani da ita don bunƙasa ilimi, da cigaban ɗan-adam.
Za a horar da malaman darasin motsa-jiki da sauran darussa, da haɗa gasannin cikin makaranta, da tsakanin makarantu, don ƙarfafa buga ƙwallo a-kai-a-kai.
Yayin da ministocin Nijar suka yaba kan zaɓar Nijar don ƙaddamar da shirin, shi ma shugaban FIFA ya yaba da aniyar Nijar ta bunƙasa harkar ƙwallo a cikin ƙasar.
Raba ƙwallo a makarantu
Ko a watan Maris da ya gabata, a wani ɓangare na shirin, FIFA ta yi rabon ƙwallo ga wasu makarantun a Nijar.
An yi rabon ƙwallayen ne a jihar Dosso, inda aka ba da kyautar ƙwallo 720 a wani biki da ya gudana ranar Litinin 17 ga Maris 2025, ƙarƙashin jagorancin gwamnan soja na Dosso, Kanal-Manjo Bana Alhassane.
Bikin ya samu halartar jami’an gwamnati da suka haɗa da shuwagabannin tsaro, da jami’an ma’aikatun ilimi da na matasa da wasanni.
Comments
No comments Yet
Comment