Dollar

40,5865

0.02 %

Euro

46,6180

-0.58 %

Gram Gold

4.301,8400

-0.88 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Nijeriya ta doke Morocco da ci 3-2 inda ta ɗauki kofin WAFCON a karo na 10

WAFCON 2024: Ƙungiyar Super Falcons ta zama Sarauniyar Ƙwallon Ƙafa a Afirka bayan ta doke Morocco

Jennifer Echegini, wadda aka shigar daga benci, ta ci ƙwallon da aka samu nasara a minti na 88 yayin bayan da Nijeriya ta farfaɗo da ci biyu da aka yi mata na farko a wasan don doke kasar Morocco mai masaukin baki da ci 3-2 a ranar Asabar a wasan ƙarshe na gasar Kofin Mata na Afirka.

Wannan nasarar a Rabat ta tabbatar da Nijeriya a matsayin sarauniyar ƙwallon ƙafa ta mata a Afirka, inda suka kafa tarihi da lashe kofin karo na 10 cikin gasanni 13.

Morocco ta sha kashi a wasan karshe karo na biyu a jere, duk da cewa sun fara jagoranci da kwallaye biyu cikin mintuna 24, amma Nijeriya ta dawo da kwallaye uku a rabin lokaci na biyu.

Esther Okoronkwo ta taka muhimmiyar rawa a nasarar Super Falcons -- ta ci kwallo ta farko, ta taimaka wajen na biyu, sannan ta bayar da bugun tazara wanda Echegini ta kammala don ba wa masu masaukin baƙin mamaki a wannan wasa mai cike da tarihi.

Morocco, tare da goyon bayan taron jama'a masu cike da kuzari a filin wasa na Stade Olympique mai kujeru 21,000 a babban birnin kasar, sun fara jagoranci a minti na 12.

Shugaba Tinubu ya yaba wa tawagar.

Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya taya Super Falcons murna bisa jajircewar da ‘yan wasan suka nuna a ranar Asabar da dare domin cin wannan kofi.

‘‘Da aiki tukuru, sadaukarwa, da jajircewa, kun cimma burin da al’ummar Nijeriya ta yi mafarki da addu’a a kai. Al’umma na jiran dawowar zakarunmu. Nijeriya na taya ku murna,’’ in ji Tinubu.

A lokacin wasan, Najeriya ta yi kuskuren kawar da ƙwallo sau da dama, inda ta fada wajen Chebbak, wadda ta zura ƙwallo mai kyau da ke tashi sama wanda bai ba wa mai tsaron gida Chiamaka Nnadozie wata dama ba ta tare ƙwallon.

Kwallon ta biyu ta shiga a mintuna 12 inda ‘yar Morocco Sanaa Mssoudy ta buga ƙwallon kaɗan ta shiga raga.

Nijeriya ta fi rike ƙwallo a rubu’in kfarko kafin a tafi hutun rabin lokaci fiye da masu masaukin baki.

Amma jagorancin Morocco ya ragu bayan mintuna 64 yayin da Okoronkwo ta yaudari Er-Rmichi daga bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan duba VAR ya nuna cewa kwallon Folashade Ijamilusi ta taba hannun Nouhaila Benzina.

Kwallon ta kara wa Nijeriya kwarin gwiwa, kuma suka farkewa mintuna bakwai daga baya lokacin da Okoronkwo ta taimaka da kwallon da Ijamilusi ta zura daga kusa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#