Dollar

40,5865

0.02 %

Euro

46,6180

-0.58 %

Gram Gold

4.301,8400

-0.88 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bryan Mbeumo mai shekaru 25, ya ci ƙwallaye 20 a wasanni 38 da ya buga wa Brentford a kakar bara.

Man United ta gabatar da Bryan Mbeumo, sabon ɗan wasanta ɗan Kamaru

Manchester United ta gabatar da Bryan Mbeumo sabon ɗan wasanta ga masoya ƙungiyar da manema labarai, bayan ya baro takwararta Brentford.

Yayin bikin gabatar da shi, ɗan wasan ɗan asalin Kamaru ya bayyana cewa, da yana yaro “ya taso yana saka jesin" Manchester United.

A ranar Litinin ne Mbeumo, mai shekaru 25 ya koma Man U kan yarjejeniyar da za ta kai shekarar 2030, tare da zaɓin ƙarin shekara guda.

Man U ta sayo ɗan wasan ne kan kimanin fam miliyan 65 (dala miliyan $87), wanda ke nuna kimarsa, kasancewar ko a kakar bara ya ciyo wa Brentford ƙwallaye 20 a wasanni 38.

‘Katafariyar ƙungiya’

Mbeumo ya ce, "Wannan katafariyar ƙungiya ce mai gagarumin filin wasa da kuma magoya baya masu nuna ƙauna. Muna da aniyar fafatawa don lashe manyan kofuna".

Baya ga Mbeumo, kocin United Ruben Amorim, ya ɗauko wasu 'yan wasa biyu a wannan bazarar domin kaucewa maimaita mummunan rashin tagomashin da United ta yi fama da shi a bara.

‘Yan wasan su ne ɗan wasan gaba na Wolves, Matheus Cunha, da matashin ɗan wasan Paraguay, Diego Leon.

Ranar Lahadi ne Manchester United za ta fara wasannin sada-zumunta na share fagen kaka mai zuwa a Amurka, inda za ta kara da West Ham a filin wasa na MetLife da ke jihar New Jersey.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#