Dollar

40,7015

0.02 %

Euro

47,2204

1.43 %

Gram Gold

4.394,9300

2.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Son zai bar Tottenham a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan ƙungiyar bayan ya buga wasanni 454 a dukkan fafatawa — wanda ya sanya shi a matsayi na bakwai cikin 'yan wasan da suka fi yawan buga wasa a tarihin ƙungiyar.

Kyaftin ɗin Tottenham Son Heung-min zai bar kulob ɗin bayan shafe shekara 10

Kyaftin ɗin Tottenham Hotspur, Son Heung-min, ya sanar da cewa zai bar ƙungiyar a wannan bazarar. Ɗan wasan ɗan asalin Koriya ta Kudu mai shekaru 33, ya koma Tottenham daga Bayer Leverkusen ta Jamus a shekarar 2015, kuma zai bar ƙungiyar bayan taimaka wa Spurs lashe gasar UEFA Europa League a kakar da ta gabata — kofin su na farko cikin shekaru 17.

Kafin wasan Tottenham da Newcastle United da za a buga a Seoul, Koriya ta Kudu, ƙasar da Son ya fito, ya bayyana cewa: “Kafin mu fara taron manema labarai, ina so in bayyana cewa na yanke shawarar barin ƙungiyar a wannan bazarar.”

Son zai bar Tottenham a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan ƙungiyar bayan ya buga wasanni 454 a dukkan fafatawa — wanda ya sanya shi a matsayi na bakwai cikin 'yan wasan da suka fi yawan buga wasa a tarihin ƙungiyar.

A cikin wannan lokaci, ya zura ƙwallaye 173, wanda hakan ya ba shi matsayi na biyar a jerin masu yawan zura ƙwallo a tarihin Spurs, inda 127 daga ciki suka kasance a gasar Premier League.

"Wannan ita ce shawarata mafi wahala cikin aikina. Ina da abubuwan tunawa masu daɗi."

"Ina bukatar sabon muhalli domin kalubalantar kaina. Ina buƙatar ɗan canji – shekaru 10 lokaci ne mai tsawo. Na iso arewacin Landan a matsayin yaro mai shekara 23, yanzu zan bar ƙungiyar a matsayin namiji cikakke kuma mai cike da alfahari."

"Ina so na gode wa dukkan magoya bayan Spurs saboda ƙauna da goyon bayan da suka bani. Ina fatan lokacin bankwana ya dace kuma wannan shi ne lokaci mafi kyau na yanke wannan shawarar. Ina fatan kowa zai fahimta kuma ya mutunta hakan."

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#