Dollar

40,7015

0.02 %

Euro

47,2204

1.43 %

Gram Gold

4.394,9300

2.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Manchester United ta Ingila ta shiga tattaunawa don dauko golan PSG ta Faransa, Gianluigi Donnarumma.

Man United za ta maye gurbin Onana da Donnarumma na PSG

Bayan da Paris Saint-Germain ta Faransa ta gaza bai wa golanta, Gianluigi Donnarumma sabuwar kwantiragi, a yanzu golan ya samu ƙungiyoyin da ke zawarcin sa ido-rufe.

Cikin ƙungiyoyin da ke fatan samun Donnarumma akwai Manchester United ta Ingila, wadda rahotanni ke cewa tuni suka shiga tattaunawa da tauraron mai tsaron gidan.

Yayin da kwantiraginsa ke ƙarewa ƙarshen kakar bana, rahotannin daga The Telegraph na cewa United ta shiga takarar ɗauko Donnarumma inda take fuskantar zazzafar takara.

Cikin masu zabarin Donnarumma akwai Al-Ittihad ta Saudiyya, da Galatasaray ta Turkiyya, waɗanda duka suka yi masa tayin albashin fam miliyan €20, daidai da £330,000 duk mako.

A yanzu PSG na da niyyar sayar da haziƙin golan ɗan asalin Italiya, don kaucewa abin da ya faru da tsohon zakaran ƙungiyar, Kylian Mbappe, wanda ya koma Real Madrid ba tare PSG ta sayar da shi ba.

Makomar Onana

A halin yanzu, golan Manchester United Andre Onana yana hutun jinya, kuma babu tabbas kan zai warke kafin fara kakar baɗi, ga shi United za ta yi wasa da Arsenal ranar 17 ga Agusta.

Wannan na cikin dalilan da United ke neman wanda zai maye gurbin Onana, wanda da ma rashin tagomashinsa ya sa an daɗe ana raɗe-raɗin cewa ƙungiyar na neman-kai da shi.

Baya ga Donnarumma, Man United na duba yiwuwar sayo Emiliano Martinez, mai tsaron gidan takwararta Aston Villa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#