Dollar

40,7086

0.17 %

Euro

47,4348

-0.19 %

Gram Gold

4.444,4400

0.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ya ce dakarun masu jajircewa sun gano tare da fasa bama-bamai sama da 14 da ‘yan ta’addan suka ɗana a wurare daban daban.

Dakarun Nijeriya sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 17 a Borno

Dakarun haɗin gwiwa na Operation Hadin Kai (OPHK), a arewa maso gabashin Nijeriya sun ce sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 17 a wasu hare-haren da suka kai a jihohin Borno da Adamawa.

Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na soji, kaftin Reuben Kovangiya, ya bayyana a wata sanarwa cewa ‘yan ta’addan suna aika-aika ne a ƙananan hukumomin Bama da Konduga da Gwoza da Magumeri da kuma Biu na jihar Borno da kuma ƙaramar hukumar Michika a jihar Adamawa.

Ya ce dakarunsu jajirtattu sun gano tare da fasa bama-bamai fiye da 14 da ‘yan ta’addan suka ɗana a wurare daban daban.

“A ci gaba da ƙoƙarin hana ‘yan ta’addan ‘yan Boko Haram da ISWAP sakewa dakarun Operation HADIN KAI (OPHK), tare da tallafin ɓangaren sojin sama na OPHK da kuma ‘yan sa-kai, sun ci gaba da kai hare-hare a arewa maso gabashin Nijeriya daga  ranar 23 ga watan Yuli zuwa ranar 2 ga wata Agusta na shekarar 2025,” in ji shi.

Ya ce  dakarun sun kwance bama-baman da aka ɗana wa fararen-hula da dakaru ba tare da wata matsala ba yayin hare-haren.

Kovangiya ya ƙara da cewa a lokacin samanen, dakarun sun taimaka wajen mayar da ‘yan gudun hijira 987 gidajensu a Mandaragrau da ke ƙaramar hukumar Biu.

“Wannan ya dace da shirin gwamnatin Jihar Borno na mayar da mutane gidajensu da kuma farfaɗo da lamuran zamantakewa da tattalin arziƙi,” in ji shi.

A cewarsa dakarun OPHK sun aiwatar da ayyuka tare da dakarun ƙasar Nijar a yankunan Diffa da Duji-Damasak, inda suka inganta tsaro da kuma kwanciyar hankali a wuraren.

“Ayyukan hare-haren waɗanda ake yi bisa umarnin shugabannin sojin sun nuna jajircewar dakarun OPHK wajen dawo da zaman lafiya a arewa maso gabashi da kuma samar da yanayin da ya dace da ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙi,”  in ji Kovangiya.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#