Sport
Dollar
40,5998
-0.12 %Euro
47,4661
0.03 %Gram Gold
4.435,1300
0.73 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wata sanarwa da hukumar ta NAFDAC ta wallafa a shafinta na X ta ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin Daraktan bincike da tilastawa na hukumar, Martins Iluyomade.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya, (NAFDAC) ta kama wasu haramtattun kayayyaki da ba a yi musu rajista ba kuma wa’adin amfaninsu ya ƙare, waɗanda darajarsu ta haura Naira biliyan 1.5 a yayin wani gagarumin aikin tabbatar da tsaro a kasuwar bajekoli ta Legas.
Wata sanarwa da hukumar ta NAFDAC ta wallafa a shafinta na X ta ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin Daraktan bincike da tilastawa na hukumar, Martins Iluyomade.
Sanarwar ta ce samamen da hukumar ta yi ya mayar da hankali ne a bangaren kayan kwalliya na kasuwar, inda aka gano wasu shaguna da dama na cike da kayan kwalliya da kayan abinci, da sauran kayayyakin da hukumar NAFDAC ta gano wadanda ba su da rajistar ko alamar kwanan wata.
“An kwashe kaya da ke maƙare a cikin tirela ɗaya, yayin da aka kama wata tirelar cike da kayan kwalliya,” kamar yadda NAFDAC ta rubuta.
Rahotanni sun ce direban tirela na biyu ya gudu, amma jami’an NAFDAC sun samu nasarar tsare motar.
Hukumar ta NAFDAC ta bayyana kamen a matsayin daya daga cikin mafi girma a watannin baya-bayan nan kuma wani bangare ne na yaki da yaduwar gurɓatattun kayayyaki a fadin kasar.
Hukumar ta ce tana ci gaba da aiwatar da ayyukanta a duk fadin kasar da nufin kare lafiyar jama’a ta hanyar kama abubuwa masu hadari a kasuwa.
Sanarwar ta kara da cewa, "Hukumar ta himmatu wajen kare lafiyar jama'a da kuma tabbatar da cewa amintattun kayayyaki kawai ake samarwa ga masu amfani a Nijeriya."
Wannan ci gaban na zuwa ne a matsayin wani bangare na kokarin da hukumar NAFDAC ke yi na kawar da gurɓatattun kayayyaki daga kasuwannin Nijeriya.
A baya-bayan nan hukumar ta bankado wani gagarumin haramtaccen aiki da ake yi da ya hada da sayar da sinadarai na jabu, da kayan abincin da wa’adin amfaninsu ya kare, da takin da ba a ba da izinin amfani da shi ba, da kuma dawo da wuraren haɗa magunguna na jabu a yankin Alapere da ke Ketu a Legas.
Iluyomade ya shaida wa manema labarai cewa harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri game da wata kungiyar masu aikata laifuka da ke aikin jabun abinci da sinadarai.
Ya bayyana matakin da hukumar ta dauka a matsayin yakin da take yi na kare lafiyar ‘yan Nijeriya, yana mai jaddada cewa mutanen da ke bayyana a matsayin halastattun ‘yan kasuwa a yayin da suke gudanar da ayyukansu, suna barazana ga lafiyar al’umma.
Comments
No comments Yet
Comment