Sport
Dollar
40,5997
-0.12 %Euro
47,4500
0 %Gram Gold
4.433,4300
0.69 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wasiƙar da lauyan shugaban EFCC, Olatimbo Ayinde, ya aika wa People Gazette ta yi gargaɗin cewa idan jaridar ba ta janye labarin kuma ta nemi afuwa ba, shugaban hukumar zai ɗauki maka ta a kotu.
Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-ƙasa, Ola Olukayode, ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya yi garkuwa da shugaban kamfanin man Nijeriya NNPC, Bashir Bayo Ojulari, tare da tilasta masa yin murabus.
Wata sanarwar da hukumar EFCC ta fitar ranar Laraba ta ce Olukayode ya bai wa jaridar Peoples Gazette da ta wallafa labarin wa’adin sa’o’i 48 ta janye labarin tare da neman afuwa a fili daga shugaban na EFCC.
A makon jiya ne jaridar ta Peoples Gazette ta wallafa wani labari inda ta ce shugaban EFCC ya yi garkuwa da shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPC, Bashir Bayo Ojulari, kuma ya tilasta masa ya yi murabus bisa umarnin wata mata mai suna Olatimbo Ayinde.
Comments
No comments Yet
Comment