Dollar

40,6141

-0.1 %

Euro

47,3988

-0.17 %

Gram Gold

4.425,3700

0.51 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kyaftin Adewusi ya tabbatar da cewa harin ta sama ya yi sanadin halaka ‘yan ta’adda da dama, sannan da dama sun ji munanan raunuka.

Sojojin Nijeriya sun tarwatsa bikin 'yan ta'adda, sun kashe 30 a jihar Zamfara

Rundunar hadin gwiwa ta sojin saman Nijeriya ta Operation FANSAN YAMMA (OPFY) ta sake samun wata gagarumar nasarar gudanar da aikinta bayan wani hari da ta kai a ranar 4 ga watan Agusta da ya gabata a wani gagarumin taromda ‘yan ta’adda da suka yi a jikin Tsaunin Asola da ke yankin Yankuzo a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation FANSAN YAMMA’ Kyaftin David Adewusi, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce sun kai hare-haren ne bisa sahihan bayanan sirri da suka nuna haduwar ‘yan ta’adda daga garuruwan Faskari da Kankara na Jihar Katsina, tare da wasu ’yan bindiga daga sassa daban-daban na Jihar Zamfara, wadanda suka taru domin bikin aure.

Kyaftin Adewusi ya tabbatar da cewa harin ta sama ya yi sanadin halaka ‘yan ta’adda da dama, sannan da dama sun ji munanan raunuka.

Ya ƙara da cewa ‘yan’uwan ‘yan ta’addan ne suka kwashe wadanda suka jikkata zuwa ƙauyen Yankuzo domin kula da lafiyarsu.

A wani samame na hadin gwiwa da suka kai, dakarun Brigade 1, karkashin sashe na 2 OPFY, sun kai farmaki ta kasa da sanyin safiyar ranar 5 ga watan Agusta.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#