Dollar

38,8085

0.01 %

Euro

43,4830

-0.01 %

Gram Gold

4.059,3900

0.14 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An wanke Fasto ɗan Nijeriya, Timothy Omotoso daga zargin aikata fyaɗe bayan da mai shri’a ya gano cewa masu gabatar da ƙara sun yi kusukure wajen shigar da ƙarar.

Afirka ta Kudu za ta dukaka kara kan wanke fasto dan Nijeriya daga zargin fyade

Masu gabatar da ƙara na Afirka ta Kudu a ranar Talata sun ce za su ɗaukaka ƙara kan wanke fastor ɗan Nijeriya daga zargin aikata fyade da wata kotu ta yi, wanda ya janyo ka-ce-na-ce a ƙasar a ‘yan watannin nan.

Kimanin mata 20 sun zargi faston da neman su, cikin su har da wadanda ke cewa ya yi musu fyaɗe, abin kunyar da ya janyo Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yin ƙorafi kan yawaitar cin zarafin mata.

A ranar Asabar aka kama Omotoso da wani laifin na daban na karya dokokin shige da fice da zargin fataucin ɗan adam.

“Ofishin Mai Gabatar da Ƙara ya ce akwai manyan dalilan da za su sanya a ɗaukaka ƙara kuma a samu nasara, duk da ruɗanin yanayn shari’ar,” in ji oifishin na gwamnati a wata sanarwa.

Binciken cikin gida

Wanke Omotoso ya janyo nuna rashin jin daɗi a faɗin Afirka ta Kudu bayan alƙalin ya gano cewa, bayanan Pastor ɗin ba su gamsar ba, su ma masu gabatar sa ƙara ba su yi abin da ya dace ba.

Mata da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a wajen kotun a Gqeberha, wanda a baya ake kira Port Elizabeth, kamar yadda hukuncin kotun ya bayyana.

A ranar Talata ofishin mai gabatar da ƙarar ya ce za su ci gaba da gudanar da binciken cikin gida kan halayyar da masu gabatar sa ƙara na farko suka nuna kan batun, kuma a watan Yuni za a fitar da rahoto.

An faɗaɗa binciken da zai haɗa da na masu gabatar da ƙara, don tabbatarwa idan ma ta kama a ɗauki matakan ladabtarwa a kan masu laifi.

‘Addu’ar neman gafara’

A shekarar 2017 ne aka fara kama fastor din ɗan shekara 66 kan zarge-zarge 32 bayan mata sun zarge shi da ɗauke su da kansa kafin ya ci zarafinsu.

Sun ce fastor ɗin zai nemi gafara bayan lalata da kowace mace, waɗanda a lokacin wasu daga cikin su suna makaranta.

Omotoso ne jagoran Cocin Jesus Dominion International (JDI), mai hedkwata a garin Durban da ke gaɓar tekun Gabashin Afirka ta Kudu.

JDI na da rassa a Nijeriya da Isra’ila, in ji gwamnatin Afirka ta Kudu.

A tsakanin 2023 da 2024 sama da mata 42,000 ne suka kai korafin an yi musu gyade ga ‘yan sandan Afirka ta Kudu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#