Ƙungiyar Iranian Red Crescent ta ce mutane 555 sun mutu a hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran, yayin da rikicin ke ci gaba da tsananta.

Adadin Mace-Mace Ya Kai 555 a Hare-Haren Amurka da Isra’ila Kan Iran

Hukumomin agaji na Iran sun ce adadin waɗanda suka rasa rayukansu a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila ya kai mutum 555. Ƙungiyar agajin gaggawa ta Iranian Red Crescent ta bayyana cewa hare-haren sun shafi aƙalla yankuna 131 a faɗin ƙasar, lamarin da ya jawo asarar rayuka mai yawa, duk da cewa ba a bayar da cikakken bayani kan adadin waɗanda suka jikkata ba.

Kamfanin dillancin labarai na Fars ya rawaito cewa sabbin alkaluman sun nuna ƙarin mace-mace idan aka kwatanta da bayanan farko da aka fitar a ranar 1 ga Maris, inda aka ce daruruwan mutane sun mutu tare da jikkata masu yawa. Sai dai har yanzu babu sabuwar sanarwa kan yawan waɗanda suka samu raunuka.

Hare-haren sun fara ne a ranar 28 ga Fabrairu lokacin da Isra’ila da Amurka suka kaddamar da farmaki kan Iran a daidai lokacin da ake tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. Daga baya Iran ta mayar da martani da kai hare-hare kan Isra’ila da wasu ƙasashen yankin da ke dauke da sansanonin Amurka.

A cikin farmakin, an kuma ba da rahoton mutuwar Jagoran Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei tare da wasu manyan jami’an gwamnati, lamarin da ya ƙara tsananta rikicin yankin.

Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#