Sport
Kakakin ma’aikatar harkokin waje ya ce shugabannin na cikin ƙoshin lafiya
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce Jagoran Addinin ƙasar Ali Khamenei da Shugaban Ƙasa Masoud Pezeshkian suna cikin aminci, yana mai watsi da iƙirarin da Amurka da Isra’ila suka yi na cewa an kashe su.
Baghaei ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na ABC News, inda ya ce shugabannin biyu na “cikin ƙoshin lafiya” kuma ana tafiyar da al’amura bisa tsari, tare da dakarun ƙasar na ci gaba da kare Iran daga hare-hare.
Tun da farko, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi iƙirarin cewa akwai bayanai da ke nuna an kashe Khamenei. Haka kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafin Truth Social cewa Khamenei ya mutu, ba tare da gabatar da hujja ba.
Baghaei ya ce waɗannan iƙirarin ba su da tushe, yana mai jaddada cewa shugabannin Iran na cikin koshin lafiya.
Tushen labari: TRT Hausa
Comments
No comments Yet
Comment