An ayyana makoki na kwanaki 40 yayin da IRGC ta yi alƙawarin ramuwar gayya

Iran Ta Sanar da Mutuwar Ayatollah Khamenei a Hari

Kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta ce an kashe Jagoran Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, a harin da Isra'ila da Amurka suka kai, lamarin da ya janyo kiraye-kiraye ga Rundunar Juyin-Juya-Hali ta ɗauki matakin ramuwar gayya.

Gidan talabijin na gwamnati ya sanar da zaman makoki na kwanaki 40 tare da bayar da hutu na kwanaki bakwai ga jama'a bayan mutuwar jagoran mai shekaru 86, wanda ya riƙe madafun iko tun 1989.

Rahotanni sun ce an kuma kashe ‘yarsa da jikarsa da kuma surukinsa a harin. Mai gabatar da labarai a gidan talabijin na gwamnati ya ce shahadar da ya yi ba za ta gusar da tafarkinsa ba, tare da jaddada ci gaba da jajircewa.

Rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta sha alwashin hukunta waɗanda ta zarga da kashe Khamenei, tana mai cewa ramuwar gayyar za ta kasance mai tsanani.

Majiyoyi sun ce an kai harin ne yayin da Khamenei ke ganawa da manyan masu ba shi shawara. Isra’ila ta yi iƙirarin cewa an kashe shi tare da wasu manyan jami’ai, ciki har da Ali Shamkhani da Mohammad Pakpour.

Tushen labari: TRT Hausa

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#