Sport
Dollar
41,1434
0.12 %Euro
48,3350
0.95 %Gram Gold
4.432,1000
0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ziyayar Shugaba Recep Tayyip Erdogan mai cike da tarihi zuwa Somalia a shekarar 2011, yayin da yake Firaminista, ta yi tasiri a zukatan mutane.
Ziyarar da Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai Somalia a shekarar 2011 wani ta kawo wani babban sauyi a makomar ƙasar, in ji wani ministan ƙasar Somalia.
Ministan tashoshin jiragen ruwa da sufirin ruwa na Somalia Abdulkadir Mohamed Nur ya sanar da kamfanin dillancin labaran Anadolu a wata zantawa cewa ziyarar Erdogan ta watan Agustan shekarar 2011 ta faru ne a ɗaya daga cikin lokuta mafi wuya a tarihin Somalia tun bayan rushewar madafun ikon ƙasar a shekarar1990.
Ziyarar Erdogan zuwa Mogadishu da maiɗakinsa Emine Erdogan da yara da ministoci aba ce da ake tunawa da ita a matsayar ranar da ba za a taɓa mantawa ba a Somalia, wadda a wancan lokacin take fama da matsanancin fari a tarihinta , in ji ta.
Jami’an Somalia sun ce wannan ziyarar ta kasance lokacin sauyi a wajen ɗauke ƙasar daga ƙaɗaici zuwa ajandar duniya, inda ta ƙarfafa dangantakar Turkiyya da Somalia zuwa wani mataki na muhimmanci.
Nur ya bayyana cewa Somalia, wadda ta kasance tamkar an yi watsi da ita a tun lokacin da gwamnatinta ta durƙushe a shekarar 1990, ta yi fama da ɗya daga cikin fari mafi tsanani a tarihinta.
Ya ƙara da cewa, "A wancan zamanin, Somaliya ƙasa ce da aka kebe daga duniya ba tare da taimako ba. A lokacin da shugaba Erdogan tare da majalisar ministocinsa, da iyalansa, da dukkan jami'ansa suka isa Somalia, wani lamari ya faru, ba wai kawai al'ummar Turkiyya na samun taimako ba, amma hankalin duniya baki daya ya karkata ga Somalia."
Nur ya jaddada cewa, Turkiyya ba ta taba ja da baya daga Somaliya ba tun bayan ziyarar Erdogan, yana mai cewa, "Tun daga wannan rana, muna samun ci gaba a kowace rana. Gudunmawar da Turkiyya ta bayar wajen sake gina Somalia na da matukar muhimmanci."
Comments
No comments Yet
Comment