Sport
Dollar
41,2792
-0.05 %Euro
49,0107
0.8 %Gram Gold
4.895,2300
0.21 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wasu masana na ganin idan ana so a magance matsalar tsaro a arewa maso yammacin Nijeriya, ya kamata gwamnatoci su yi sulhu da ‘yan bindiga a yankin, yayin da wasu ke ganin sulhu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba.
Ɓarayin daji sun sace mutum 43 daga wani masallaci da ke ƙauyen Gidan Turbe, a ƙaramar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara da ke arewacin Nijeriya.
Kazalika rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 12 a ƙauyen Godai na ƙaramar hukumar Bukkuyum da ke Jihar a ranar Lahadi.
Lamuran dai sun faru ne a lokacin da shugabannin al’umma da wasu ‘yan bindiga a jihar Katsina mai maƙwabtaka suka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan ta’addar.
Wasu masana na ganin idan ana son a magance matsalar tsaro a arewa maso yammacin Nijeriya, ya kamata gwamnatoci su yi sulhu da ‘yan bindiga a yankin, yayin da wasu ke ganin sulhu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba.
Harin da aka kai kan masallacin na jihar Zamfara ya faru ne da kimanin ƙarfe 5:30 a lokacin da ake sallar asuba. Rohotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi wa masallacin ƙawanya kuma suka yi awon gaba da masallata 43 inda suka nufi Dutsen Gahori da su.
Jiragen yaƙin Nijeriya sun yi luguden wuta a sansanonin ƴan ta'adda a Zamfara
Dutsen Gahori da ke ƙaramar hukumar Tsafe, yana cikin dokar daji da yake wani ɓangare na jihar Zamfara da wasu ɓangarori na jihar Kebbi har zuwa Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Comments
No comments Yet
Comment