Sport
Dollar
41,3071
0.03 %Euro
48,7945
0.38 %Gram Gold
4.905,1700
0.42 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa hauhawar farashin ta ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 daga kashi 21.88 cikin 100 da ta kasance a watan Yuli.
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu a karo na biyar a jere a watan Agustan shekarar 2025, lamarin da zai kawo sassauci ga mutanen da ke fama da tsadar rayuwa, in ji hukumomin ƙasar.
Alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa hauhawar farashin ta ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 daga kashi 21.88 cikin 100 da ta kasance a watan Yuli.
Alƙaluman sun nuna raguwa na kashi 1.76 cikin 100 daga wata zuwa wata, abin da ke nuna gagarumar raguwa daga kashi 32.15 cikin 100 da aka samu a watan Agustan shekarar 2024.
Alƙaluman, da ke bibiyar yadda matsakaicin farashin kayayyakin yau da kullum ke sauyawa, sun bayya cewa farashin kayayyaki sun ƙaru da maki 126.8 a watan Agusta daga maki 125.9 a watan Yuli.
An samu sassaucin hauhawar farashin kayayyaki a Afrilu a Nijeriya – NBS
Hauhawar farashi ta wata-wata ta tsaya a kashi 0.74 cikin 100, ƙasa da kashi 1.99 cikin 100 na watan Yuli, lamarin da ke ishara ga raguwar hauhawar farashi a faɗin ƙasar.
Comments
No comments Yet
Comment