Dollar

41,2917

-0.01 %

Euro

48,7832

0.35 %

Gram Gold

4.898,3000

0.28 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban Turkiyya ya jaddada ‘‘goyon bayan ƙasarsa’’ ga Qatar, yana mai Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan tawagar Hamas a Doha kana ya bayyana hakan da ‘‘ta’addanci da ya kai wani mataki na daban’’.

A shirye Turkiyya take ta taimaka wa ƙasashe ‘yan’uwanta da ƙarfin tsaro: Erdogan

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga al'ummar Musulmai a faɗin duniya da su ƙara matsa lamba kan Isra'ila, yana mai cewa dole ne a yi amfani da matakan tattalin arziki wajen rage ƙarfin Tel Aviv.

"Dole ne mu ƙara kaimi a fannin diflomasiyya don ƙara ƙaƙaba wa Isra'ila takunkumi," in ji Erdogan, yana mai gargaɗin cewa manufar gwamnatin Netanyahu ita ce "ci gaba da kisan kiyashi da ƙare-dangi a Falasɗinu tare da haifar da rashin kwanciyar hankali a yankin".

Da yake jawabi a wajen taron ƙasashen Larabawa da Musulmai da aka gudanar a birnin Doha a ranar Litinin, shugaban na Turkiyya ya jaddada cewa ƙasashen Musulmai suna da ‘dama da kuma ƙarfin hana Isra’ila cim ma manufarta ta faɗaɗa ikonta a yankin’’, yayin da ya yi tir da abin da ya bayyana a matsayin ‘tsarin ta’addancin Isra’ila na tayar da hankali da zubar da jini’’.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#