Dollar

42,3350

0.2 %

Euro

49,1712

0.05 %

Gram Gold

5.547,4900

-0.07 %

Quarter Gold

9.430,0100

0 %

Silver

69,2000

0.51 %

Mutuwar yara 23 a yankin Kordofan ta nuna yadda ake da matuƙar buƙatar kayan jinƙai a ƙasar da ke arewa maso gabashin Afirka, inda yunwa ke ƙaruwa bayan fiye da watanni 30 na yaki.

Yaƙin Sudan: Fiye da yara 20 sun mutu sakamakon tsananin rashin abinci a cikin wata guda

Fiye da yara ashirin sun mutu saboda matsalolin ƙarancin abinci a cikin wata guda a tsakiyar Sudan, inda rikici mai ƙarfi tsakanin sojojin ƙasar da rundunar RSF ke ci gaba da tayar da hankali, in ji wata ƙungiyar lafiya.

Mutuwar yara 23 a yankin Kordofan ta nuna yadda ake da matuƙar buƙatar kayan jinƙai a ƙasar da ke arewa maso gabashin Afirka, inda yunwa ke ƙaruwa bayan fiye da watanni 30 na yaki.

Sudan ta faɗa cikin ruɗani a watan Afrilun 2023 lokacin da rikicin neman iko tsakanin sojoji da rundunar Rapid Support Forces (RSF) ya ƙara ƙazancewa a babban birnin Khartoum da sauran sassan ƙasar.

A cewar ƙididdigar Majalisar Ɗinkin Duniya, yaƙin ya kashe fiye da mutane 40,000, amma ƙungiyoyin agaji suna cewa wannan adadin ya zarta haka inda ta ce akwai yiwuwar adadin ya wuce haka sosai.

A cewar ƙwararrun masu nazarin yunwa na duniya, zuwa watan Satumba an jefa kusan mutum 370,000 cikin yunwa a Kordofan da yammacin Sudan zuwa Satumba yayin da wasu miliyan 3.6 ke dab da faɗawa cikin tsananin yunwa, kamar yadda ƙwararrun suka bayyana.

Sudan Doctors Network, ƙungiyar kwararru da ke bibiyar rikicin, ta ce an ruwaito mutuwar yaran tsakanin 20 ga Oktoba da 20 ga Nuwamba a garin Kadugli da garuruwan Dilling da aka yi wa ƙawanya

A ranar Juma’a, ƙungiyar ta ce mutuwar ta kasance "sakamakon tsananin rashin abinci da ƙarancin kayayyakin masarufi" a wuraren biyu, inda takunkumi "ke hana shigowar abinci da magunguna kuma ke sanya rayukan dubban fararen hula cikin haɗari."

Kadugli, babban birnin lardin Kordofan ta Kudu,shi ne inda aka bayyana yunwa a farkon wannan watan ta hanyar Integrated Food Security Phase Classification (tsarin tantance matakin tsaro na abinci).

RSF ta kewaye garin Kadugli tsawon watanni, tare da dubban mutane suna makale yayin da rundunar ke ƙoƙarin karɓar ƙarin yankuna daga hannun sojojin Sudan.

Fadan neman iko da Kordofan ya ƙara ƙarfi a farkon wannan shekara bayan sojoji sun tilasta RSF ta fice daga Khartoum.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#