Dollar

42,3350

0.2 %

Euro

49,1712

0.05 %

Gram Gold

5.547,4900

-0.07 %

Quarter Gold

9.430,0100

0 %

Silver

69,2000

0.51 %

A yayin wannan taron wanda jigonsa zai kasance 'hadin kai, daidaito da ɗorewa', shi ne taron G20 na farko da aka taba gudanarwa a nahiyar Afrika, kuma zai mayar da hankali kan sassauta bashi ga ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi.

An ƙaddamar da taron shugabannin ƙasashen G20 a Afirka ta Kudu

An fara taron shugabannin ƙungiyar G20 a Johannesburg da ke Afrika ta Kudu, inda shugaban ƙasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya gabatar da jawabi na farko yayin da wakilai suka hallara don tattaunawa ta tsawon kwanaki biyu.

A yayin wannan taron wanda jigonsa zai kasance 'hadin kai, daidaito da ɗorewa', shi ne taron G20 na farko da aka taba gudanarwa a nahiyar Afrika, kuma zai mayar da hankali kan sassauta bashi ga ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi — wata babbar matsala da ke hana ci gaba kasashen da ke tasowa.

Shugabannin za su kuma tattauna yadda za a samu daidaito kan sauyin yanayi da sauya zuwa hanyoyin samar da makamashi masu tsafta, tare da sauran muhimman manufofi.

Ajandar ta kunshi tattaunawa kan hadin kai na ciki da kuma hanyar dabarun kungiyar, yayin da aka shirya shugabannin su gudanar da jerin ganawa-biyu a gefe a lokacin wannan taron na kwanaki biyu.

Amurka ba za ta halarci taron G20 ba

Ministan Harkokin Wajen Afrika ta Kudu, Ronald Lamola, ya ce a wannan makon ana sa ran kasashe 42 za su halarci wannan taron na tarihi na G20 da kasar ke karɓar baƙunci.

Amurka, wacce ta kasance daya daga cikin kasashen da suka kafa G20, ta yi watsi da halartar taron bana.

A farkon wannan watan, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa ba zai aika jami'in Amurka zuwa Johannesburg don taron ba, inda ya zargi Afrika ta Kudu da 'tauye hakkin ɗan’adam kan al'ummar al’ummar ‘yan Afrikaana farar fata — ikirarin da gwamnatin Afrika ta Kudu ta musanta sau da yawa cewa ba su da tushe.

A wannan shekara, dangantaka tsakanin Washington da Pretoria ta kai mafi karancin mataki saboda bambance-bambance a kan manufofin waje da na cikin gida.

An kafa G20 a 1999, kuma ta kunshi kasashe 19 da kungiyoyi na yanki guda biyu — Tarayyar Turai (EU) da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU).

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#