Wasu mayaƙa da ke da alaƙa da RSF sun ɓalle tare da shiga Rundunar Sojin Sudan. Kwamandan mayaƙan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan ya ga “masifu” a cikin RSF, tare da yin kira ga sauran mayaƙan ƙungiyar da su ajiye makamansu su koma gida.
Wata ƙungiyar mayaƙa mai alaƙa da Rundunar RSF ta ta balle daga ƙungiyar a ranar Jumma’a tare da shiga Rundunar Sojin Sudan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran gwamnatin Sudan, SUNA, ya ruwaito.
Al-Tayeb Mohammed Ahmed ne ya jagoranci rundunar, wanda aka fi sani da Al-Tayeb Al-Wahido.
Manyan jami’ai daga rundunar sojin Sudan da Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa ne suka karɓi sojojin da suka balle.
A cikin wata sanarwa ga manema labarai, Al-Wahido ya bayyana cewa ya fice daga RSF tare da shiga rundunar sojin Sudan ne bayan da ya ga “masifu” da ke faruwa a cikin mayaƙan ƙungiyar.
Ya yi kira ga mambobin RSF da su shiga rundunar sojin, su “koma gida” tare da sake duba matsayinsu, yana mai cewa “babu wata manufa da za ta tabbatar da ci gaba da yaƙin.”
Har yanzu RSF ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan mataki ba.
Ficewar ta baya-bayan nan ta biyo bayan wasu jerin sauya sheƙa irin waɗannan da mayaƙan na RSF suka yi a kwanakin baya. A ranar 31 ga Agusta, kusan mayaƙan RSF 200, ciki har da manyan kwamandojin fagen daga, suka ɓalle tare da shiga Rundunar Sojin Sudan a Omdurman, inda suka zo da kayan aikin yaƙi.
Tun da farko, a ranar 19 ga Agusta, rundunar sojin ta ce jami’an RSF 318, ciki har da kwamandoji huɗu, sun ɓalle tare da motoci masu sulke har 50.
A ranar 13 ga Agusta, hukumomin Sudan sun sanar da cewa kwamandoji 21 da mayaƙa 270 sun shiga rundunar sojin tare da motoci 37 na yaƙi.
Sudan na cikin yaƙi tsakanin rundunar sojin ƙasar da RSF tun daga watan Afrilun 2023. Rikicin ya kashe dubun-dubatar mutane tare da tilasta wa miliyoyin wasu barin gidajensu.