Sport
Dollar
41,2910
0.2 %Euro
48,4340
0.61 %Gram Gold
4.758,6800
1.43 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Firaministan Faransa Fancois Bayrou na fuskantar barazanar rasa kujerarsa bayan ‘yan adawa sun haɗa kai wajen tunkarar gwamnati ta tsiraru a zaɓen watan gobe.
Kimanin kashi 63 cikin 100 na mutanen Faransa suna son a rusa majalisar dokokin ƙasar tare da neman a sake sabon zaɓe, in ji ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a da kamfanin IFOP ya yi wa gidan talabijin ɗin LCI TV ranar Laraba, yayin da Firaminista Francois Bayrou ke ƙoƙarin kare gwamnati ta ‘yan tsiraru.
Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a da kamfanin IFOP ya gudanar ta ji ra’ayin mutane 1,000 ta hanyar intanet ranar 26 ga watan Agusta.
Bisa ga alamu za a kayar da gwamnatin ‘yan tsiraru ta Bayrou a watan gobe bayan manyan jam’iyyun adawa— daga masu ra’ayin riƙau zuwa ra’ayin ‘yan mazan jiya — sun ce ba za su goya masa baya ba a zaɓen da Bayrou ya sanar da cewa za a yi ranar 8 ga watan Satumba, kan shirye-shiryensa na rage kasafin kuɗi sosai.
Comments
No comments Yet
Comment