Dollar

41,2549

0.23 %

Euro

48,1939

0.23 %

Gram Gold

4.713,1600

0.46 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A makon jiya ne Shugaban Amurka Donald Trump ya soke tallafin da Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da shi na dala biliyan 4.9 da ƙasar ke bai wa ƙasashen waje.

Rundunar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu da DRC na fuskantar ƙarancin kuɗaɗen tallafi: MDD

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya na fuskantar matsanancin ƙarancin kuɗaɗen tallafi kuma matakin da Amurka ta ɗauka na iya taƙaita ƙarfin kare fararen-hula a wurare kamar Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, in ji mai magana da yawun rundunar ta MDD a ranar Talata.

A makon jiya ne Shugaban Amurka Donald Trump ya soke tallafin dala biliyan 4.9 da ƙasar ke bai wa ƙasashen waje wanda Majalisar Dokokin Amurka ta amince da shi.

Kuɗaɗen sun haɗa da dala miliyan 800 na ayyukan wanzar da zaman lafiya da aka ware na shekarar 2024 da 2025, a cewar saƙon gwamnatin Trump ga Majalisar.

Tuni dai ofishin kasafin kuɗi na Fadar White House ya ba da shawarar yanke kuɗaɗen da ake ware wa ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD na shekarar 2026, saboda gazawar ayyukan a ƙasashen Mali da Lebanon da kuma Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Kongo.

Washington dai ta kasance a kan gaba wajen bayar da gudunmawa, inda take ba da kashi 27 na biliyan 5.6 na kasafin da ake ware wa ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ayyukan MDD kan wanzar da zaman lafiya 11 na aiki

"Idan babu isassun kayan aiki, ba za mu iya yin aiki sosai ba, kuma hakan zai yi tasiri sosai wajen gurgunta ayyukan zaman lafiya da tsaro a wurare kamar Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, inda rashin kuɗaɗe zai iya shafar ƙarfinmu wajen kare fararen-hula,’’ in ji mai magana da yawun tawagar wanzar da zaman lafiya na MDD a New York.

“Muna kira ga ɗaukacin ƙasashe mambobin ƙungiyar da su bayar da gudunmawarsu ga aikin wanzar da zaman lafiya kuma a kan lokaci don ci gaba da gudanar da muhimman ayyuka da za su yi tasiri ga samar da zaman lafiya,’’ in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#