Dollar

41,2910

0.2 %

Euro

48,4340

0.61 %

Gram Gold

4.758,6800

1.43 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bisa wata ƙuri’ar jin ra’ayi da aka yi ta intanet, an gano cewa kaso 60 na matasa ‘yan Gen Z na Amurka waɗanda ke tsakanin shekara 18 zuwa 24 na nuna goyon bayansu ga ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas a yaƙin da Isra’ila ke yi da ita a Gaza.

Bincike ya gano cewa 6 cikin 10 na matasan Amurka na goyon bayan Hamas kan Isra’ila

Wani sabon bincike ya gano cewa kashi 60 cikin 100 na matasan Gen Z a Amurka suna goyon bayan ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas, fiye da Isra'ila a yaƙin da ake yi a Gaza.

A cikin jerin tambayoyi da aka yi, an tambayi masu amsa ta intanet: "A rikicin Isra'ila da Hamas, wa kuka fi goyon baya, Isra'ila ko Hamas?"

A cewar binciken da aka fitar a wannan makon, kashi 60 cikin 100 na matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 24 sun nuna goyon baya ga Hamas fiye da Isra'ila.

Daga cikin rukunin shekarun da suka fi goyon bayan Isra'ila akwai masu shekaru 25-34 da kashi 65 cikin 100, 35-44 da kashi 70 cikin 100, 45-54 da kashi 74 cikin 100, 55-64 da kashi 84 cikin 100, da kuma masu shekaru 65 da sama da kashi 89 cikin 100.

Binciken ya kuma gano cewa masu kada kuri'a sun kasu gida biyu kan ko Isra'ila tana aikata kisan kare dangi a Gaza, inda aka samu kunnen doki wato 50-50

Damuwa kan hakkokin dan Adam na Falasdinawa

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#